logo

HAUSA

Akwai bukatar gaggauta dakatar da bude wuta da yaki a yankin Gabas ta Tsakiya

2024-10-28 20:48:27 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen Sin ta ce jerin abubuwan dake faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya a baya-bayan nan, ya sake jadadda bukatar gaggawa ta dakatar da bude wuta da yake-yake.

Kakakin ma’aikatar Lin Jian ne ya bayyana haka yau, yayin taron manema labarai na kullum, a lokacin da yake amsa tambaya game da hare-haren Isra’ila kan sansanonin sojin Iran a ranar 26 ga wata.

A cewar Lin Jian, Sin na adawa da keta ’yanci da tsaron kasashe da kuma amfani da karfi. Ya ce ana cikin mawuyacin yanayi a yankin Gabas ta Tsakiya, kuma ya kamata dukkan bangarori su kaucewa ta’azzarar barazanar tsaro a baki dayan yankin.

Lin Jian ya kuma soki zargin kafafen yada labaran Amurka dake cewa, Sin na gudanar da ayyukan leken asiri. Ya ce Amurka ba ta taba daina leken asirin kasar Sin ba, yana cewa, Amurka ta dade tana gudanar da ayyuka masu yawa na sauraron bayanai ko satar bayanan sirri na kawayenta a fadin duniya, yayin da take zargin sauran kasashe da aikata hakan. Bugu da kari, kakakin ya bukaci Amurka ta dakatar da munanan ayyukan nan take, ta kuma daina tayar da rikici da hargitsi a duniya. (Fa’iza Mustapha)