logo

HAUSA

Bangarorin masana’antu da kasuwancin kasar Sin sun bayyana adawa da matakan kariyar ciniki da kasar Amurka ta dauka

2024-10-28 14:03:20 CMG Hausa

A yayin taron manema labaran da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira a yau Litinin, mataimakin shugaban hukumar raya cinikayya a tsakanin kasar Sin da kasashen duniya wato CCPIT, Zhang Shaogang, ya amsa tambayoyi game da wasu matakan kariyar ciniki dake shafar kasar Sin wadanda kasar Amurka ta fitar a kwanan baya.

Mr. Zhang ya ce, kwanan baya, kasar Amurka, da kungiyar tarayyar kasashen Turai wato EU, sun ci gaba da gabatar da wasu matakan kariyar ciniki dake shafar kasar Sin, wadanda suka saba da ka’idar kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO, lamarin da ya haddasa barazana ga tsarin samar da hajoji a tsakanin kasa da kasa.

Ya ce a madadin dukkan bangarorin masana’antu da kasuwancin kasar Sin, Hukumar CCPIT, da Kungiyar kasuwanci ta kasar Sin wato CCOIC, suna matukar adawa da wadannan matakai. A sa’i daya kuma, sun yi kira ga kasar Amurka, da kungiyar EU, da su mutunta ka’idojin kasuwannin duniya, da ka’idar yin takara cikin adalci, kana su dakatar da matakan da ba su dace ba nan take.

Zhang ya jaddada cewa, wannan ba kiran bangarorin masana’antu da kasuwanci daga kasar Sin kadai ba ne, har ma kira ne daga kasashen duniya.

A yayin taron majalisar tattauna harkokin masana’antu da kasuwanci na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik na shekarar 2024 karo na 3, wakilan harkokin masana’antu da kasuwanci na Sin da Amurka, sun gabatar da daftarin hadin gwiwa, domin sa kaimi da a zartas da ka’idojin hadin gwiwa kan tsarin samar da hajoji na yankin Asiya da Pasifik, inda aka gabatar da bukatun bude kofa, da yin hadin gwiwa kan tsarin samar da hajoji a tsakanin kasa da kasa, yayin da ake bin ka’idojin kungiyar WTO da dai sauransu. Hakan ya nuna fatan bangarorin masana’antu da kasuwanci na kasashen duniya, ciki har da na Sin da Amurka. (Mai Fassara: Maryam Yang)