logo

HAUSA

Zhou Haiyan dake jagorantar manoman garinsu wajen bude sabuwar hanyar kara samun kudin shiga

2024-10-28 15:30:48 CMG Hausa

A kauyen Yilite dake birnin Ulanhot, na jihar Mongoliya ta gida mai cin gashin kanta dake arewacin kasar Sin, akwai wani wurin musamman da aka yiwa lakabi da “Daular Dawisu”, wanda ba aljanna ce kadai ga dawisu ba, har ma wata sabuwar duniya ce ga mazauna kauyen, domin suna kara samun kudin shiga da wadata. Wadda ta kirkiro wannan duka ita ce Zhou Haiyan, wadda aka fi sani da “Sarauniyar Dawisu”. Mace ce da ta yi amfani da hazaka, don mayar da aikin kiwon dawisu a matsayin wata hanyar samun wadata ga mazauna kauyen na Yilite.

Mu’amalar dake tsakanin Zhou Haiyan da tsuntsayen dawisu, ta samo asali ne daga kiran waya da ta yi da kawunta. A lokacin, kawun nata ya bayyana mata a waya cewa, yana cin kwan dawisu, wanda nan take ya tada sha’awar Zhou Haiyan. Ta ji cewa wannan tsuntsu da ke zama a kudu na iya haifar da wata kima a arewa, don haka ta fito da ra’ayin kiwon dawisu, kuma ta yanke shawarar daukar wannan a matsayin jagorar kasuwancinta.

Sai dai shawarar da Zhou Haiyan ta yanke ba ta samu tallafi daga ’yan uwa da abokan ta ba. A ganin su, tun zamanin can can can da, dawisu tsuntsu ne dake rayuwa a kudu maso gabas, don haka suna ganin ta ina za su iya rayuwa a arewa maso gabas? Amma Zhou Haiyan ta yi imanin cewa, dawisu suna da kyan gani sosai, ta yadda kowa da kowa ke son kallonsu, tabbas za a iya samun damar yin kasuwanci a cikin abubuwan da kowa ke sha’awarsu. Don haka, ta kama kan hanyar kasuwanci ta kiwon dawisu ko ta halin kaka.

A shekara ta 2010, Zhou Haiyan ta kai ’yar uwarta zuwa lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, don yin bincike, ta kuma kashe RMB yuan dubu 50, kwatankwacin dalar Amurka sama da dubu 7, don sayen dawisu guda 10. Ba tare da bata lokaci ba, ta yi hayar mota ta dauki dawisun zuwa gida.

Amma, hanyar gudanar da kasuwanci ba ta da kyau, ba kamar yadda ta yi tsamani ba.

Bayan an shiga lokacin kaka da lokacin sanyi, yanayi yana ta kara yin sanyi, bisa ga irin halin da ake ciki, dawisu sun soma nuna alamun gajiya, har ma sun soma mutuwa daya bayan daya. Baya ga haka, gidan dawisu da ta shagaltu da ginawa a lokacin zafi, ya ruguje sakamakon matsalar gidauniyar.

Duk da ta fuskanci irin wannan matsala, Zhou Haiyan ba ta yi kasa a gwiwa ba. Ta gano cewa, mutuwar kashin farko na dawisu ya samo asali ne sakamakon bambance-bambancen yanayin zafi, don haka ta gyara tsarin kiwo, kuma ta kara sayen wasu dawisu guda 50.

Ko da yake aikin kiwo ya tafi cikin kwanciyar hankali a wannan karon, amma dawisu kanana da aka kyankyashe sun yi fama da ciwon nakasa, ko kuma sun mutu bayan an kyankyashe su. Bayan yin la'akari sosai, Zhou Haiyan ta yi hasashen cewa, watakila, matsalar na da nasaba da harawa. Don haka, ta fara ziyartar wasu kwararrun masu kiwo, tana kuma karanta littattafai, da kuma tuntubar bayanai. Bayan kokarin da ta yi cikin watanni shida, ta bullo da dabarar ciyar da dawisu. A shekara ta biyu, ta yi nasarar kyankyashe gungun dawisu kanana masu lafiya.

Amma, kaddara ko da yaushe kamar tana wasa da Zhou Haiyan. Bayan kiwon wadannan dawisu sama da wata guda, fiye da 100 daga cikinsu beraye sun cije su har sun mutu cikin dare. Abun da ya sa Zhou Haiyan ta kusan fadowa.

Ta tuno abin da ya faru a lokacin, ta ce “Ni da kanwata duk mun rude, muka kwanta kwana uku ba ci ba sha.”

Jajircewa da imanin da Zhou Haiyan take da su, sun ba ta damar sake tashi tsaye. Ta gayyaci kwararru don yi mata jagora, tare da tsarawa, da inganta gidan dawisu bisa ga yanayin sanyi na musamman a arewa. A lokaci guda kuma, ta kuma mai da hankali kan kimar abinci mai gina jiki ta hanyar kimiyya. A karshe, an yi nasarar kyankyashe gungun dawisu da suka dace da yanayin arewa. Wannan ya nuna wani sabon mafari da fata ga sana’ar kiwon dawisu na Zhou Haiyan.

Bayan tsawon lokaci, sana’ar kiwon dawisu ta Zhou Haiyan sannu a hankali ta fara samun saurin ci gaba. A kowace shekara, ’yan kasuwa daga kudu suna zuwa don sayen ’ya’yan dawisu. Idan aka kwatanta da dawisu na kudu, dawisu na arewa ba sa saurin kamuwa da cututtuka, kuma suna da gashin fuka-fukai. Zhou Haiyan ta yi amfani da damar don fadada girman kiwo, tare da kafa kungiyar hadin kai ta kiwon dawisu ta birnin Ulanhot. Haka kuma, tana ba da ’ya’yan dawisu, da tallafin fasaha ga manoman da suka shiga kungiyar, don jagorantar kowa da kowa wajen samun wadata tare.

A lokacin aikin kiwon dawisu, Zhou Haiyan ta gano cewa, a duk lokacin da aka yi asarar dawisu, za a iya amfani da su sosai.Yayin aikin kiwon dawisu, Zhou Haiyan ta gano cewa, za a iya cin gajiya daga duk wata asara ta asali da dawisu ke iya fuskanta. Ba ta so ta rika jefar da dawisu da suka mutu, a maimakon haka, ta rika ajiye gashinsu don yin samfurori. A cewar Zhou Haiyan, “A daya bangaren kuma, ana iya mayar da abu mara amfani zuwa taska, kana ana iya kiyaye kyawun dawisu.” Samfuran dawisu da ta yi masu kama da rayayyu, suna biyan bukatun masu yawon bude ido. Wannan kuma ya kara baiwa lambun dawisun ta wata hanya ta daban ta samun kudin shiga.

Baya ga samfurin dawisu, Zhou Haiyan ta kuma kera wasu kayayyakin gashin fuka-fukan dawisu, kamar su lambobi, da tsintsiya, da rigar kai, da ’yan kunne, da fanfo, da abin rufe fuska, da dai sauransu, wadanda suka samu karbuwa sosai.

Zhou Haiyan ta ce, domin kara amfani da gashin dawisu yadda ya kamata, sau da yawa tana zuwa sauran yankuna domin kara samun ilmi, da kuma yin nazari kan fasahar kera kayayyakin fasaha na gashi. Bisa kokarin da take yi, sannu a hankali ta mallaki wannan fasaha, kuma ta yi nasarar neman aikin gadon al’adun gargajiya na wurin.

Bayan cimma nasarar gudanar da kasuwanci, Zhou Haiyan ta fara tunanin yadda za a taimakawa karin mazauna kauyen, wajen kama turbar samun wadata. Ta fara ba da horon fasahar samar da gashin fukafukin kyauta ga manoman wurin. Ya zuwa yanzu, mutanen da suka samu horo daga wajen ta sun wuce 3600. Matan karkara da mutanen da suke da bukatu na musamman da dama, sun samu aikin yi, da karuwar kudin shiga ta hanyar sana’ar kiwon dawisu ta Zhou Haiyan. Zhou Haiyan ta shimfida wata hanya ta samun farin ciki da wadata, wadda ta baiwa mutane da yawa damar ganin makoma mai kyau a nan gaba.