Kasar Sin ta bada tallafin abinci ga mabukata da na kudin karatu ga dalibai a Malawi
2024-10-27 15:50:57 CMG Hausa
Kasar Sin ta bayar da tallafin garin masara da wake ga gidauniyar Shaping Our Future Foundation (SOFF) ta Monica Chakwera, uwargidan shugaban kasar Malawi, domin tallafawa ’yan kasar dake fama da rashin abinci a yankin Nkhotakota dake bakin tafki.
Haka kuma, gwamnatin kasar Sin ta bayar da tallafin kudin karatu ga gidauniyar ta hannun shirin tallafin karatu na jakadan kasar Sin, domin tallafawa dalibai mabukata da gidauniyar ke kula da su.
Babban jami’in kula da harkokin ofishin jakadancin Sin a Malawi, Wang Hao ne ya gabatar da gudunmuwar ga uwargidan shugaban kasar a fadar Kazumu dake Lilongwe, babban birnin Malawi, yayin wani biki da ya samu halartar jami’an ofishin jakadancin Sin da na gwamnatin Malawi da ma jami’an gidauniyar SOFF.
A cewar Wang hao, tallafin abincin ya biyo bayan sanarwa da matakin ta-baci da shugaban kasar Lazarus Chakwera ya yi kan gundumomi 23 ciki har da Nkhotakota, da kuma kiran samar da tallafin jin kai ga miliyoyin al’ummar kasar dake fama da yunwa. (Fa’iza Mustapha)