logo

HAUSA

Ribar masana’antun Sin ta zarce Yuan triliyan 5 a watanni tara na farkon bana

2024-10-27 16:14:36 CMG Hausa

Yau Lahadi, hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fidda bayani cewa, tsakanin wata Janairu zuwa watan Satumban bana, ribar masana’antun kasar Sin ta kai Yuan triliyan 5 da biliyan 228 da miliyan 160, adadin da ya ragu da kaso 3.5 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin a bara.

An gamu da raguwar ribar masana’antu tsakanin watan Janairu zuwa watan Satumba na bana, sakamakon wasu matsalolin, amma, jimillar ribar masana’antu da aka samu ta zarce Yuan tiliyan 5, kana, ribar da aka samu a fannin sabbin sana’o’in masana’antu, kamar kira ta fasahohin dake kan gaba, tana karuwa da sauri, lamarin da ya nuna karfin bunkasuwar tattalin arzikin masana’antu.

A cewar hukumar, duk da ribar masana’antun kasar Sin ta ragu, sabbin sana’o’in masana’antu suna bunkasuwa cikin yanayin mai karko. Haka zalika, za a farfado da ribar kamfanonin masana’antu sakamakon karkon harkokin masana’antu da tabbaci kan bunkasuwar masana’antun. (Mai Fassara: Maryam Yang)