logo

HAUSA

Iran ta ce tana da hakkin mayar da martani ga harin Isra’ila

2024-10-27 16:10:07 CMG Hausa

Kasar Iran ta bayyana cewa, tana da hakki halaltacce kuma bisa doron doka na mayar da martani ga harin da Isra’ila ta kai jiya, kan wurare da dama a larduna 3 na kasar.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na sashen hulda da jama’a na rundunar sojin Iran ta ruwaito babban hafsan sojin kasar na cewa, da safiyar jiya Asabar, jirgin yakin Isra’ila ya harba makamai masu linzami dake cin dogon zango dauke da kananan ababen fashewa, zuwa yankunan kan iyaka na lardin Ilam dake yammacin kasar da lardin Khuzestan na kudu maso yammaci da kuma kewayen babban birnin kasar Tehran.

Sanarwar ta kara da cewa, harin bai yi ta’adi mai yawa kan kayayyakin sa ido na sojin kasar ba. Kuma tsarin tsaron sararin samaniya na Iran din, ya kakkabo wani adadi mai yawa na makamai masu linzami tare da kare jirgin yakin makiya daga shiga sararin samaniyar kasar.

Da safiyar jiya Asabar, rundunar tsaron Isra’ila ta ce ta kaddamar da hare hare ta sama, daidai kan wasu wurare a yankuna daban daban na Iran, a matsayin martani ga hare haren da Iran din ta kai mata a watannin baya-bayan nan. A ranar 1 ga watan Oktoba, Iran ta harba makamai masu linzami kimanin 180 kan wasu wurare a Isra’ila. (Fa’iza Mustapha)