logo

HAUSA

Adadin filin noma mai fadin hecta miliyan 30 ne ba a aikatawa a yanzu haka a tarayyar Najeriya

2024-10-27 15:53:39 CMG Hausa

Karamin minista a ma`aikatar gona ta tarayyar Najeriya Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya tabbatar da cewa a kalla hecta miliyan 30 na filin noma ne ba`a aikatawa yanzu haka a Najeriya.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ranar Juma`a 25 ga wata a birnin Abuja lokacin da yake karbar bakuncin shugaban kungiyar manoman tumatir na Najeriya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ya ci gaba da bayanin cewa a kalla Najeriya na da fili mai arzikin noma da ya kai fadin hecta miliyan 73, amma daga cikin wannan adadi ana iya sarrafa hecta miliyan 41 zuwa 43 ne kadai, wannan ya nuna cewa ana asarar kusan rabin adadin filayen noman da ake da su a kasar.

Kamar yadda ministan ya fada, gaza noma wannan adadi na fili ya taka rawa sosai wajen haifar da matsalolin karancin abinci a cikin Nijeriya, lamarin da kuma ya haddasa tsadar farashin kayan abincin gaba daya.

Karamin ministan gonar na tarayyar Najeriya ya jaddada bukatar hanzartar shawo kan wannan matsala musamman a lokacin aikin noman rani dake tafe.

Sanata Aliyu Abdullahi ya yi kira ga shugabannin kungiyar manoman tumatir na kasa cewa, duk da sana`ar tasu tana da muhimmanci ga ci gaban tattalin arzikin kasa, amma yana fatan cewa hakan ba zai dauke hankalin su daga rungumar noman abinci ba domin kare al`umma daga fuskantar matsalar yunwa.

A jawabinsa shugaban kungiyar Alhaji Abdullahi Ringim kira ya yi ga ma`aikatar gonar ta tarayya da ta yi kokari wajen maganin matsalolin da suke hana aiwatar da manufofin kasa a game da aikin noman tumatir.

Manufofin kamar yadda ya fada sun hada da batun samar da wadatattun kudade a bangaren bunkasa noman tumatir, da maganin yawan kwari dake damun tumatirin, kana kuma da rage tsadar kudin dakon tumatirin a duk lokacin da za a yi sufurin sa zuwa sassa daban daban na Najeriya.(Garba Abdullahi Bagwai)