logo

HAUSA

An yi jana’izar tsohon faraminista Hama Amadou a kauyensa na Youri

2024-10-26 12:00:42 CMG Hausa

A ranar jiya Juma’a 25 ga watan Oktoban shekarar 2024, aka yi jana’izar tsohon faraminista kuma tsohon shugaban majalisar dokokin Nijar, Hama Amadou a kauyen da aka haife shi na Youri mai tazarar kilomita 34 daga birnin Yamai da ke cikin yankin Tillabery, ‘yan Nijar sun nuna alhininsu har zuwa kabarinsa.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Bikin nuna juyayi da alhini, da karramawa ga tsohon shugaban majalisar dokoki, kana tsohon faraminista Hama Amadou ya gudana a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai, inda shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, kana shugaban kasa Abdourahamane Tiani ya jagoranci bikin nuna alhinin da karramawa a hukumance, kamar yadda dokokin kasa suka tanada a irin wannan muhimmin lokaci, ga mutumin da ya bautawa kasa, kamar marigayi Hama Amadou, wannan kuma a gaban idon mambobin kwamitin ceton kasa, mambobin gwamnati, jakadun kasashen waje da ke Nijar, iyalan mamacin, da abokai da aminan arziki.

Tsoffin shugabannin kasa da suka hada da Mahamane Ousmane da Salou Djibo, Seyni Oumarou tsohon shugaban majalisar dokoki, sun halarci wannan bikin nuna alhini.

Gaban gawar mamacin da ke lullube da tutar kasar Nijar, daya bayan daya, shugaban kasa Abdourahamane Tiani da sauran manyan jami’ai suka tsaya gaban gawar mamacin domin yi masa adu’o’in neman kyautata makomarsa, da neman gafarar Allah, domin saka shi aljannar Firdausi.

Dubun dubatar mutane da ayarin motoci da babura suka rakiyar gawar tsohon faraminista Hama Amadou har zuwa kauyensa na Youri, inda aka yi jana’izarsa a cikin wani gandun gidansa. (Mamane Ada)