logo

HAUSA

Isra’ila ta kammala hare haren ramuwar gayya kan wasu sassan kasar Iran

2024-10-26 15:08:45 CMG Hausa

Rundunar tsaron kasar Isra’ila ko IDF, ta ce ta kammala hare hare da ta yi niyyar kaiwa wasu sassan kasar Iran, a matsayin ramuwar gayyar hare haren da Iran din ta kaddamar kan wasu yankunan ta cikin watannin baya bayan nan.

Wata sanarwa da IDF din ta fitar da sanyin safiyar Asabar din nan, ta ce

an harba wasu makamai ta sama zuwa wurare da aka tsara a yankuna daban daban na Iran, ciki har da wuraren kirar makamai masu linzami, da wasu na’urorin kakkabo makamai masu linzami daga samaniya, da karin wasu na’urori dake taimakawa Iran din kaddamar da hare hare ta sama.

A na ta bangaren kuwa, helkwatar tsaron sararin samaniyar Iran, ta ce ta yi nasarar kakkabo makaman da Isra’ila ta harba, in ban da wasu kalilan da suka yi ta’adi a wasu sassa, kuma ana gudanar da bincike kan hakan, kamar dai yadda kafar kamfanin dillancin labarai ta kasar Tasnim ta bayyana. (Saminu Alhassan)