logo

HAUSA

An kaddamar da aikin hanyar motar da ta taso daga Sokoto zuwa Badagry a jihar Legos bayan shekaru 40 da kirkirar aikin

2024-10-26 12:10:44 CMG Hausa

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin fara aikin hanyar motar da ta taso daga Sokoto zuwa Badagry a jihar Legos domin saukaka harkokin sufuri tsakanin jahohin dake shiyyar kudu maso yamma da kuma arewa maso yammacin Najeriya.

A jiya juma’a 25 ga wata ne aka kaddamar da aikin a garin Gulumbe dake yankin karamar hukumar Birnin Kebbi a jihar Kebbi, kuma an tsara kammala kashi na farko na aikin cikin shekaru biyu masu zuwa.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

A lokacin dayake jawabi yayin bikin kaddamar da aikin hanyar a madadin shugaban kasa, gwamnan jihar Kebbi Alhaji Nasir Idris, ya ce aikin hanyar zai taimaka mutuka gaya wajen kara daga darajar dukkannin garuruwan da ke shiyoyin biyu da ma sauran sassan kasa.

Kamar yadda yake kunshe cikin jawabin na shugaban kasa, gwamanti ta samar da kudade isassu domin gudanar da aikin don tabbatar da ganin ba a samu tsaiko ba wajen gudanar da shi.

Shugaban na tarayyar Najeriya a ta bakin gwamnan jihar ta Kebbi ya ce aikin mai nisan kilomita 1,068 an kirkire shi ne tun a 1980 zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Shehu Shagari, inda a wancan lokaci aka tsara fara aikin daga Legos amma yanzu aka fara daga Sokoto.

A jawabin sa ministan ayyukan na Najeriya Mr Dave Umahi ya ce kashi na fako na aikin wanda ya kunshi gina madatsun ruwa guda 68 domin aikin noman rani za a kammala cikin shekaru 2.

Ministan ya ce za a samar da madatsun ruwan ne a kan hanyar da za a gina wanda zai taimaka sosai musamman ga manoman dake garuruwan da aikin titin zai keto ta wajen, wannan ce ta sanya ma gwamnati tsara samar da filiyen noma masu yawa a hanyar.

Ministan kasafi da tsare-tsare Alhaji Atiku Bagudu da gwamnan jihar Sokoto suna daga cikin wadanda suka shaida bikin kaddamar da aikin hanyar.(Garba Abdullahi Bagwai)