logo

HAUSA

An yi taro karo na shida tsakanin rukunoni masu kula da ayyukan tattalin arziki na kasashen Sin da Amurka

2024-10-26 16:27:39 CMG Hausa

Yayin da yake halartar taron shekara-shekara na bankin duniya, da asasun ba da lamuni na duniya wato IMF, a jiya Juma’a a birnin Washington na kasar Amruka, mataimakin ministan kudin kasar Sin Liao Min, da takwaransa na kasar Amurka, Jay Shambaugh, sun jagoranci taro na shida, na rukunonin kasashen biyu masu kula da harkokin tattalin arziki.

Bangarorin Sin da Amurka, sun zurfafa shawarwari a wasu batutuwa da dama, ciki har da babban yanayin tattalin arziki da kasashen biyu ke ciki, gami da manufofin tattalin arzikinsu, da shawo kan kalubalen duniya, da hada gwiwa don taimakawa kasashe masu karancin kudin shiga, wajen tinkarar kalubale da sauransu.

Kasar Sin ta mai da hankali wajen gabatar da sabbin manufofin da ta bullo da su kwanan nan domin inganta tattalin arziki, da nuna damuwarta kan kara buga harajin kwastam da Amurka ta yi, kan wasu hajojin kasar ta Sin. (Murtala Zhang)