logo

HAUSA

Sin ta fitar da karfe tan miliyan 80.71 a rubu’i 3 na farkon shekarar nan

2024-10-26 15:45:55 CMG Hausa

Wasu rahotanni daga kungiyar kamfanonin sarrafa karafa ta kasar Sin, na cewa cikin rubu’i 3 na farkon shekarar nan ta 2024, Sin ta fitar da karafa da aka tono, da tatacce, da yawan sa ya kai tan miliyan 80.71, duk kuwa da tangal tangal din kasuwa, da sauye sauye a yanayin cinikayyar kasa da kasa.

Kungiyar ta ce sashen samar da karafa na Sin na samun ci gaban hada hadar fitar da karfe bisa daidaito, a wa’anin watannin 9 na farkon shekarar bana, lamarin da ya shaida karfin juriyar sashen, da ikon sa na tunkarar sabbin kalubale.

Bayanai sun nuna cewa, a tsakanin wa’adin, Sin ta fitar da tan miliyan 80.71 na karfe, wanda ya nuna karuwar kaso 21.2 bisa dari a shekara. A lokaci guda kuma, sashen masana’antun sarrafa karafa na Sin, na gaggauta ingiza kwazon sa ga amfani da fasahohin zamani, da samun ci gaba ta amfani da na’urori masu kwakwalwa, da fasahohi marasa gurbata yanayi.

Ya zuwa 8 ga watan Oktoba, kamfanonin sashen 159 sun kammala, ko sun kusa kammala sauyi zuwa fasahar fitar da mafi karantar abubuwa masu gurbata yanayi, da kafa tsarin lura da hakan.

Bugu da kari, an tsara wani shiri na musamman a wannan fanni, wanda zai tabbatar da cewa, ya zuwa karshen shekarar 2025, za a cimma nasarar sauya akalar kamfanonin kasar Sin, zuwa masu fitar da mafi karantar abubuwa masu dumama yanayi a sassa daban daban na rayuwa. A lokaci guda kuma, za a kara azamar ingiza sauya karfin samar da hajoji, a kaso sama da 80 bisa dari na kamfanonin sarrafa karafa dake sassa daban daban na kasar. (Saminu Alhassan)