logo

HAUSA

Sin da EU sun sake jaddada aniyar warware takaddama game da cinikayyar ababen hawa masu amfani da lantarki kirar Sin

2024-10-25 20:02:58 CMG Hausa

Kasar Sin da kungiyar tarayyar Turai ta EU, sun sake jaddada aniyarsu ta warware takaddamar cinikayyar ababen hawa masu amfani da lantarki kirar kasar Sin ta hanyar tattaunawa, bayan da EUn ta ce za ta gudanar da bincike, don gane da zargin samar da rangwame ga masana’antun kirar ababen hawan masu aiki da lantarki na Sin.

Wata sanarwa da ma’aikatar cinikayya ta Sin ta fitar, bayan zantawa ta kafar bidiyo, tsakanin ministan cinikayya na Sin Wang Wentao, da mataimakin babban shugaban hukumar gudanarwar EU, kuma kwamishinan kasuwanci na kungiyar Valdis Dombrovskis, ta ce sassan biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa don cimma matsayar farashi, a matsayin hanyar shawo kan takaddamar. (Saminu Alhassan)