logo

HAUSA

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayar da umarnin kamo rikakken dan bindigan nan Bello Turji dake jihar Zamfara

2024-10-25 09:53:42 CMG Hausa

 

Ministan tsaron tarayyar Najeriya Alhaji Muhammad Abubakar Badaru ya umarci dakarun sojin da suke yaki da ’yan bindiga a jihar Zamfara da su gaggauta kamo rikakken jagoran ’yan ta’adda Bello Turji.

Ministan ya bayar da umarnin ne da yammacin jiya Alhamis 24 ga wata a garin Gusau, fadar gwmanatin jihar Zamfara yayin wata ziyara daya kai jihar.

Daga tarayyar Najeriya wkailinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

A lokacin da yake jawabi ga dakarun sojin dake hedikwatar runduna ta 1, ministan ya shaida musu cewa shugaban kasa yana bibiyar ayyukan da suke gudanarwa a jihar tare kuma da nasarorin da suke samu a yaki da ’yan ta’adda a shiyyar baki daya duk da cewa dai har yanzu akwai ’yan kalubale.

Ministan tsaron na Najeriya ya ce, yana da kwarin gwiwar cewa dakarun suna da kwarewa da dabarun da za su iya kamo kasurgumin dan fashin dajin nan Bello Turji wanda ya addabi yankin tare da yaransa.

Kwamandan rundunar tsaron hadin gwiwa na yaki da ’yan ta’adda a shiyyar arewa maso yamma Major Janaral Oluyinka Olalekan shi ne ya tare ministan yayin wannan ziyara, daga bisani kuma ya ziyarci gwamnan jihar ta Zamfara Alhaji Dauda Lawan. (Garba Abdullahi Bagwai)