Kamfanin CATL na kasar Sin ya kaddamar da sabon batir na motoci masu amfani da tagwaitaccen makamashi
2024-10-25 13:40:37 CMG Hausa
A jiya Alhamis ne kamfanin kera batir na zamani na kasar Sin wato Amperex Technology ko CATL a takaice, ya kaddamar da wani sabon batiri na motoci masu amfani da tagwaitaccen makamashi ko hybrid a turance.
Babban jami’in fasaha na kamfanin CATL, Gao Huan, ya bayyana cewa, batirin wanda aka fi sani da Freevoy, shi ne batiri na farko a duniya wanda aka tagwaita kuma yana iya tafiyar kilomita 400, kana yana daukar caji da matukar sauri, kuma cajin minti 10 kacal zai iya kara nisan tuki sama da kilomita 280.
Ta hanyar hada baturan sodium-ion da na lithium-ion, Freevoy ya magance matsalar sanyin batir dake tattare da motocin sabbin makamashi (NEVs), yana kuma ba su damar yin aiki a cikin yanayin tsananin sanyi, kana yana iya sakin makamashi a yanayin sanyin digiri 40 kasa da sifiri a ma’aunin Celsius, da yin caji a yanayin sanyin digiri 30 kasa da sifiri a ma’aunin Celsius.
Motoci masu amfani da tagwaitaccen makamashi na samun tagomashi daga karin masu sayen motoci Sinawa, saboda ana iya yin doguwar tafiya da su fiye da motoci masu amfani da lantarki zalla, kuma sun fi motoci masu amfani da man fetur saukin kudi. (Yahaya)