logo

HAUSA

Najeriya na kashe dala biliyan 1.5 a duk shekara wajen shigo da madarar shanu da sauran kayayyakin da ake yi da damara cikin kasar

2024-10-25 09:57:23 CMG Hausa

 

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce, watsi da tun farko aka yi da bangaren kiwo ya sanya Najeriya dogaro kachokan wajen shigo da madara daga kasashen ketare.

Ya bayyana hakan ne jiya Alhamis 24 ga wata a birnin Abuja yayin taron wayar da kai na masu ruwa da tsaki a game da sake fasalin harkokin kiwon dabbobi a kasar wanda aka gudanar a babban dakin taro dake fadar shugaban kasa, inda ya ce, lokaci ya yi da ya kamata a ce an sauya al’amura.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce, kamar yadda bincike ya nuna a duk shekara Najeriya na kashe a kalla dala biliyan 1.2 zuwa biliyan 1.5 a duk shekara wajen odar madara zuwa cikin kasar saboda wanda ake samarwa a cikin gida ba ya iya biyan bukatun miliyoyin al’ummar kasa.

Shugaban na tarayyar Najeriya wanda ya bayyana kiwon a matsayin daya daga cikin bangarorin da suke bayar da gudummawa ga ci gaban samuwar kudaden shiga na cikin gida. Ya yi alkawarin cewa, gwamnatinsa za ta yi bakin kokarin ganin cewa ta samar da kyakkyawan yanayi da zai tabbatar da bunkasar harkokin kiwon dabbobi a dukkan matakai.

Ya ce, ya ji dadin kasancewarsa daya daga cikin mahalarta wannan taro inda ya yi albishir da cewa, ba da jimawa bangaren zai samu karuwa masu zuba jari ’yan kasa da na kasashen waje, lamarin da zai samar da kafofin aikin yi daban daban. (Garba Abdullahi Bagwai)