Sin ba za ta canza matsayarta game da mayar da hankali kan kasashe masu tasowa ba
2024-10-25 20:36:45 CMG Hausa
Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian, ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Ya ce, Sin ta dade tana kasancewa daya daga kasashe masu saurin ci gaba da masu tasowa na duniya, don haka hadin gwiwar ta da kasashen, shi ne tushen dangantakar dake tsakanin Sin da kasashen waje. Lin Jian ya ce bangaren Sin, zai ci gaba da habaka ingantacciyar bunkasuwa, ta “hadin gwiwar babban dandalin BRICS”, tare da sauran kasashe masu tasowa.
Jami’in ya kara da cewa, yammacin kasashen duniya kamar Amurka, sun riga sun kakaba takunkumi ga kasar Zimbabwe ba bisa ka’ida ba cikin tsawon shekaru fiye da 20, wanda hakan ya lalata ikon ci gaban al’ummar kasar. Game da hakan, bangaren Sin ya sake yin kira ga wasu kasashe, da kungiyoyi, da su daina kakaba takunkumi ba bisa ka’ida ba kan kasar Zimbabwe.
Don gane da babban zaben kasar Mozambique kuwa, Lin Jian ya bayyana cewa, kasar Sin ta ji dadin yadda kasar ta yi nasarar gudanar da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, da na kananan hukumomi, kana ta taya jam'iyyar Frelimo, da zababben shugaban kasar Daniel Chapo murnar samun nasara.
Game da batun Taiwan, Lin Jian ya ce a matsayin bangare da ba za a iya raba shi da kasar Sin ba, yankin Taiwan ba shi da ko wane dalili, ko iko na shiga MDD, da ma sauran kungiyoyin kasa da kasa wadanda kasashe masu ikon mulkin kai kadai suke iya shiga.(Safiyah Ma)