logo

HAUSA

Kamfanin Orano na Faransa ya dakatar da aikin samar da Uranium a Nijar

2024-10-25 10:03:48 CMG Hausa

 

A jamhuriyyar Nijar, kamafanin Faransa na Orano ya sanar jiya Alhamis 24 ga watan Oktoban shekarar 2024 da dakatar da aikin hakar karfen Uranium a wannan kasa dake yammacin Afrika da sojoji suke mulki tun yau da kusan watanni goma sha biyar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya duba mana wannan matsala tsakanin Orano da CNSP, ga kuma rahoton da ya hada mana.

 

Ta wata sanarwa ce, kamfanin kasar Faransa Orano dake Nijar, da ya shahara kan harkokin nukiliya, ya bayyana cewa zai dakatar da aikinsa na samar da karfen Uranium a Nijar daga ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2024.

Kamfanin Orano ya nuna cewa akwai matukar wahala ya ci gaba aiki cikin wannan kasa dake yammacin Afrika da sojoji suke mulki, in ji sanarwar.

Tsanantar matsalolin kudi na kamfanin Somair da Orano yake rike da kashi 68 cikin 100, sannan kamfanin dake kula da ma’adinai na Nijar dake kashi 36 cikin 100 ya tilastawa kamfanin Faransa dakatar da ayyukansa, in ji kakakin Orano.

A cewar Orano, aikin hakar Uranium a sansanin da ke Arlit a yankin arewacin Nijar na Agadez, zai tsaya daga ranar 31 ga watan Oktoba, ganin halin rashin fitar da karfen daga kasar Nijar.

A cewar shugabannin Orano, duk da kokarin da suka yi na daidaita rikicin cikin ruwan sanyi tare da sabbin hukumomin Nijar domin samun takardun izinin fitar da Uranium ya sha ruwa.

Kana, iyaka tsakanin Nijar da Benin na har yanzu rufe, kuma kokarin fita da shi ta jiragen sama ta hanyar ratsawa ta kasar Namibiya, shi ma har yanzu sojojin Nijar ba su ba da amsa mai kyau ba.

A cikin watan Juni ne, Nijar ta janye lasisin hakar Uranium na Imouraren, da aka kiyasta zuwa ton 200,000.

Har zuwa lokacin da nike hada wannan rahoto, hukumomin Nijar ba su ce kome ba, kan wannan mataki na Orano.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.