logo

HAUSA

Jami’i: Sojojin Najeriya sun kashe ’yan bindiga a kalla 140 a makon da ya gabata

2024-10-25 10:10:30 CMG Hausa

Rundunar sojin Najeriya ta ce, a kalla ’yan binga 140 ne sojojin kasar suka kashe a hare-haren da suka kai kan ’yan ta’adda a fadin kasar a makon da ya gabata.

Kakakin rundunar, Edward Buba ne ya bayyana hakan a jiya Alhamis a taron manema labarai a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, inda ya ce, sojojin sun kama ’yan bindiga 135 a mabambantan hare-haren da suka kai a makon. Kuma an kubutar da mutane 76 da aka yi garkuwa da su daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su, kazalika, sojojin sun kuma kwato makamai iri-iri har 241 da alburusai 3,245.

Buba ya kara da cewa “Ayyukan yaki da ta’addanci da ’yan tada kayar baya da sojojin ke ci gaba da yi, ya yi matukar tasiri ga rage karfin ’yan ta’adda,” inda ya bayyana cewa, sojojin sun hana kungiyoyin masu aikata miyagun laifuka cimma manufofinsu. (Yahaya)