logo

HAUSA

Ga wasu muhimman makamai masu linzami samfurin DF-26B na kasar Sin

2024-10-25 10:18:00 CGTN Hausa

A ranar 19 ga watan nan, babban kwamandan rundunar sojin kasar Sin ya yi rangadi a wani sansanin rundunar soja na makamai masu linzami. Ga wasu muhimman makamai masu linzami samfurin DF-26B, tare da wasu manyan motocin dauka da kuma harba su. An ce, irin wannan makamai masu linzami samfurin DF-26B masu cin dogon zango, su ne maganin babban jirgin ruwan dakon jiragen saman yaki. (Sanusi Chen)