logo

HAUSA

NGUEMA ANGUE NATIVIDAD EYANG: Yin karatu a Sin buri na ne tun ina karama

2024-10-25 17:59:55 CMG Hausa

Tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Equatorial Guinea, sama da rabin karni da ya gabata, duk da yadda al’amuran kasa da kasa ke sauyawa, kasashen biyu sun kasance tare da juna, suna taimakawa juna a ko da yaushe. A kan batutuwan da suka shafi muhimman muradunsu, suna ci gaba da nuna goyon baya ga juna, wanda hakan ya samar da alakar abokantaka mai karfi da dorewa tsakanin su. A shekarar bana, an daga matsayin dangantakar kasashen biyu zuwa dangantakar abokantaka ta hadin-gwiwa bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni, wanda ya sa dangantakarsu ta shiga wani sabon mataki.

Wata ’yar kasar Equatorial Guinea mai suna NGUEMA ANGUE NATIVIDAD EYANG, ta ce tun tana karama take son al’adun kasar Sin. Ta kammala karatunta a jami’ar Central South ta Sin a wannan shekara, inda ta karanci ilmin injiniyan manhajoji. Labarin NATIVIDAD na neman ilimi a kasar Sin ba kawai shaida ce ta ci gaban kanta ba, har ma ya zamo wani kyakkyawan misali na hadin kai tsakanin Sin da Afirka. A shirinmu na yau, za mu dubi labarin wannan matashiya ’yar kasar Equatorial Guinea mai suna NGUEMA ANGUE NATIVIDAD EYANG da Sin.