logo

HAUSA

Wani mai larurar gani ya haskaka yayin tseren fanfalaki na birnin Tianjin

2024-10-24 13:44:06 CRI

Cikin tsawon sa’o’i 2 da mintuna 7, matashi Li Zezhou dan shekaru 17 a duniya, wanda ke da matsayi na 2 na larurar gani, ya kammala tseren da ya gudana ranar Lahadin karshen makon jiya, a gasar tseren fanfalaki ko “Marathon” ta shekarar 2024 da aka yi a birnin Tianjin. Matashi Li ya kammala tseren rabin zango na Marathon a karon farko na shigarsa irin wannan gasa.

Matashin ya ce "Duk da cewa bana gani da idanu na, shewar da masu kallo suka rika yi min ta faranta rai na. Ina godiya da goyon bayan da sauran ‘yan tsere suka nuna min, komai ya tafi yadda ya dace".

Li, wanda dalibi ne a wata makarantar dalibai masu larurar gani dake birnin Tianjin, ya shiga gasar ta wannan karo ne tare da wasu daliban masu irin larurarsa su 5.

Yan Zhuang, shugaban kungiyar Red Cross sashen gidauniyar kula da walwalar masu tsere na birnin Tianjin, ya jagoranci bikin taya matasan murnar kammala tseren a karshen layin gasar. Inda ya ce "Ba tare da la’akari da sakamakon karshe ba, matasan sun nuna matukar hazaka".

Ga mutane masu larurar gani, kwazon su na kawar da tsaro shi ne muhimmin mataki. Don haka ne ma wannan gidauniya ta birnin Tianjin karkashin kungiyar Red Cross, ta yi hayar kwararru masu taya su tsere, tare da shirya musu horo na musamman tun a makarantar su kafin ma su kai ga halartar gasar.

Yan, ya kara da cewa, “Duk dan wasan tsere mai larurar gani yana tare da a kalla ‘yan tsere 3 masu yi masa rakiya, mafi muhimmancin su shi ne wanda zai rikewa dan tseren igiyar dake yi masa jagora, domin shi ne ke baiwa dan tseren karfin gwiwar kara sauri, da rage sauri, da sauya kwana bisa tanadin alamomin da aka sanya a kan hanyar tseren. Sauran masu rakiyar kuwa, su ne ke ba shi kariya, da sama masa taimakon abubuwan bukata daga baya da kuma gaba.

Wang Lan, daya ce daga masu yiwa ‘yan tseren rakiya, wadda kuma ke da kwarewa ta shekaru 4 a fannin, ta kuma ce "A wurare masu sarkakiya, mu ne idanun su. Sun mallaka mana zukatan su. Muna amincewa da juna".

Wannan ne karon farko da ta yi rakiyar dan tsere mai larurar gani, kuma hakan ya kara mata fahimtar yanayin mutane masu wannan larura. Ta ce "Kafin yanzu, ban taba zato marasa gani, dake fuskantar matsaloli daban daban a rayuwar yau da kullum, za su iya yin tseren marathon ba."

Ita ma Cai Cheng, mai wannan larura ta gani da aka haife ta cikin shekarun 1990, take kuma rike da mukamin shugaban wani kamfani mai samar da hidimomin gida ga jama’a, ta kammala tseren rabin marathon cikin sa’o’i 3 da mintuna 5.

A cewar ta "Watanni 2 kacal na samu, domin yin atisayen shiga wannan gasa ta marathon, kuma na sadaukar da kwazo na a wannan gasa ga Wang, da sauran ‘yan tsere na kamfanin mu. Alal hakika, bana yawan samun lokacin motsa jiki amma duk da haka na shiga wannan gasa".

Ga ‘yan wasan tsere da ke shiga gasar marathon, karfafa musu gwiwa na yin tasiri wajen ingiza kwazon su, amma ga wadanda ke shiga wasan a karon farko irin su Cai, yawan hakan na dakile kwazon su. A cewar Cai, “Kafin gasar ta dan ji kafar ta na ciwo, amma duk da haka ta dage sosai. Da na fice daga gasar kafin kammalawa, da ban kyautawa sauran ‘yan tsere na kamfanin mu ba, saboda goyon bayan da suka nuna mun har karshen gasar. Dole na gama tseren domin su”.

Domin taimakawa Cai ta kai gaci, Wang da sauran masu tsere sun rika yi mata magana, suna karfafa masa gwiwa, tare da kara mata natsuwa. A cewar ta "Ta hanyar rike igiyar, tsoro na ya gushe, kana na ji saukin damuwa, kuma ya zuwa kilomitar karshe, na manta ma da ciwon da jiki na ke yi". Daga karshe Cai ta tsallake layin kammala gasar inda masu taimaka mata suka rungume ta cikin murna.

A cewar ta "A baya ina mayar da hankali ga sakamako, amma a wannan karo, na mayar da hankali baki daya ga taimakawa sauran ‘yan wasa. Don haka na ji yanayin ya yi daban. Aiki ne mai tattare da kalubale, wato yin nawa tseren da kuma karfafa gwiwar sauran ‘yan tsere. Mutane da dama sun zo domin karfafawa masu larurar gani gwiwa yayin tseren, wanda hakan ke nuna jama’a da yawa suna mayar da hankali ga rukunonin al’umma dake kokarin inganta kwazon su. Don haka mu ma ya kamata su mayar da hankali sosai ga abubuwan da za mu iya yi musu. Wata kila muna iya farawa da tabbatar da cewa, duk hanyar da masu larurar gani ke bi ba ta dauke da wasu abubuwa da za a iya yin karo da su”.

‘Yan kasar Kenya sun lashe gasar tseren Marathon ta Suining

‘Yan wasan tsere na kasar Kenya, sun lashe lambobin yabo na gasar tseren Marathon na garin Suining dake lardin Sichuan, a kusu maso yammacin kasar Sin. Yayin gasar ta Lahadin karshen mako, dan wasan tsere Kyeva Cosmas Mutuku, ya ni nasarar lashe kambin gasar ajin maza, bayan ya kammala gudu cikin sa’o’i 2 da mintuna 18 da dakika 28, yayin da Gladys Jepkorir Kiprotich ta lashe gasar ajin mata, bayan ta kammala tseren cikin sa’o’i 2 da mintuna 37 da dakika 56.

A bangaren maza na gasar rabin marathon, dan wasan kasar Sin Zhou Youfa ne ya yi nasarar zama na daya, yayin da a ajin mata na wannan zango, ‘yar wasan kasar Kenya Brigid Jelimo Kabergei ta lashe lambar zinari.