logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da shugabannin Masar da Iran

2024-10-24 11:04:50 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah al Sisi a daren jiya Laraba a Kazan na Rasha, yayin da yake halartar taron shugabannin BRICS.

Xi ya taya Masar murnar shiga taron a matsayin mamba a karon farko. Ya kuma jaddada cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara azama wajen raya dangantakarsu zuwa huldar kafa kyakkyawar makomarsu ta bai daya a zabon zamani. Sin na fatan kara hadin gwiwa da Masar don ingiza bunkasuwar kasashen BRICS mai dorewa da karfafa karfin kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa, da ma kiyaye muradun kasashe masu tasowa.

A nasa bangaren, Abdel Fattah al Sisi ya nuna godiya ga goyon bayan da Sin ta nunawa kasarsa wajen shiga tsarin BRICS. Yana mai fatan kara tuntubar kasashen biyu a mabambantan bangarori, da ma kiyaye muradun kasashe masu tasowa da masu saurin bunkasuwa cikin hadin kai, da kuma ingiza kafa tsarin daidaita harkokin duniya bisa adalci da daidaici.

Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi musanyar ra’ayi game da halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya. A ganin Xi, batun Palasdinu muhimmin batu ne ga matsalar gabas ta tsakiya. Abin da ake sa gaba shi ne, a yi iyakacin kokarin aiwatar da kudurorin da aka zartas a yayin tarukan kwamitin sulhu na MDD, da gaggauta tsagaita bude wuta a wurin. Tabbatar da tsarin “kafa kasashe biyu” ita ce hanya daya tilo da za a bi wajen warware wannan matsala bisa adalci a duk fannoni mai dorewa.

Kazalika, an ba da labari cewa, a wannan rana da yamma, Xi ya gana da takwaransa na kasar Iran Masoud Pezeshkian. Yayin ganawar tasu, Xi ya nanata cewa, Sin ba za ta sauya matsayinta na sada zumunta da hadin gwiwarta da Iran ba, duk da sauye-sauyen yanayi da ake fuskanta a shiyya-shiyya da ma duk duniya baki daya. A nasa bangaren kuwa, Pezeshkian ya ce, Iran na fatan ita da kasar Sin za su goyi wa juna baya kan wasu muradu masu tushe na kasashen biyu, da ma yaki da babakere tare. Yana godiya ga goyon bayan da Sin take nunawa kasar na shiga tsarin BRICS. Yana mai fatan kara hadin gwiwarta da Sin mai zurfi a dandaloli masu gudanar da harkoki tsakanin bangarori daban-daban ciki har da BRICS. (Amina Xu)