logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD ya yi Allah wadai da harin ta’addaci da aka kai kan kamfanin masana’antun sararin samaniya na Turkiyya

2024-10-24 10:52:12 CMG Hausa

 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin ta’addanci da aka kai kan kamfanin masana’antun sararin samaniyar kasar Turkiyya da ke birnin Ankara.

Mataimakin kakakin sakatare janar na MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan jiya Laraba a taron manema labarai, inda ya ce, Guterres ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya cikin gaggawa.

Kazalika, ministan harkokin cikin gida na kasar Turkiyya Ali Yerlikaya ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu akalla mutane hudu ne suka mutu sa’an nan wasu 14 suka jikkata, uku daga cikinsu na cikin mawuyacin hali sakamakon harin ta’addaci da aka kai kan gine-ginen samar da kaya na kamfanin masana’antun sararin samaniyar Turkiyya da ke Ankara. (Yahaya)