logo

HAUSA

Shugabannin BRICS sun amince da sanarwar hadin gwiwa bayan taro

2024-10-24 11:11:05 CMG Hausa

Bayan taron kolin shugabannin BRICS da ya gudana jiya Laraba a birnin Kazan na kasar Rasha, shugabannin kasashen BRICS sun fitar da sanarwar hadin gwiwa da ta kunshi batutuwa da dama, kama daga yin kwaskwarima ga Majalisar Dinkin Duniya, zuwa rikice-rikicen da duniya ke fama da su.

Shugabannin sun nanata yin Allah wadai da duk wani nau’in ta’addanci tare da yin kira da a gaggauta amincewa da cikakkiyar yarjejeniyar yaki da ta’addanci a MDD. 

Kana kasashen BRICS sun yi kira ga MDD da ta taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar duniya a harkokin kirkirarriyar basira wato AI, tare da yin muhimman gyare-gyare.  

Sanarwar ta kuma mayar da hankali kan rikice-rikicen da ake fama da su a duniya, da suka hada da na yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasar Ukraine, inda shugabannin suka bayyana matukar damuwa game da tashe-tashen hankula a zirin Gaza tare da yin kira da a gaggauta tsagaita wuta da dakatar da duk wani tashin hankali. (Yahaya)