logo

HAUSA

Me Najeriya za ta iya samu daga tsarin BRICS?

2024-10-24 17:58:24 CMG Hausa

Ana ci gaba da gudanar da taron ganawa tsakanin shugabannin kasashe mambobin BRICS a birnin Kazan na kasar Rasha yanzu. A nata bangare, kasar Najeriya ta bayyana niyyarta ta shiga cikin tsarin BRICS har sau da dama. Na tuna a taron FOCAC da ya gudana a Beijing na Sin a watan Satumba da ya gabata, Yusuf Tuggar, ministan harkokin wajen kasar Najeriya ya ce, "Ba wanda zai iya hana Najeriya shiga cikin tsarin BRICS, ganin yadda kasar ta girma, kuma ta iya yanke shawara da ita kanta kan wane ne za ta yi hadin gwiwa."

Sai dai me tsarin BRICS zai haifarwa Najeriya, idan ta shiga cikin tsarin? Za mu iya samun amsa dangane da tambayar, cikin jawabin da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya yi a taron kolin BRICS na wannan karo.

Jawabin shugaba Xi ya nuna alkiblar da tsarin BRICS ya dosa, da matsaya daya da mahalarta taron BRICS na wannan karo suka cimma, wanda ya kunshi wasu kalmomi masu muhimmanci, wato su: zaman lafiya, da ci gaba, da hadin gwiwa, da adalci, da kirkiro sabbin fasahohi, da kare muhalli, gami da cudanyar al'adu.

Da farko dai, yadda aka jaddada muhimmancin zaman lafiya, ya nuna cewa, kasashe mambobin BRICS sun fi son tattaunawa maimakon fada. Saboda haka, idan kasar Najeriya ta samu damar shiga cikin tsarin BRICS, to, ba ya nufi ta dauki wani bangare don takara ko fada da wasu. Maimakon haka, za ta samu karin damammakin hadin kai don tabbatar da tsaronta, da na yankin da take ciki.

Na biyu shi ne, batun ci gaban tattalin arziki. Ta yaya tsarin BRICS zai iya taimakawa kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba mai dorewa? Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana ayyukan da kasar Sin ta yi a wannan fanni, misali kafa cibiyar raya fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI, ta Sin da BRICS, da habaka hadin gwiwar da take yi tare da sauran mambobin BRICS ta fuskar masana'antu mai nasaba da fasahohin kare muhalli, da dai sauransu. Saboda haka, idan Najeriya ta shiga cikin tsarin hadin kai na BRICS, to, za ta samu damar raya wadannan bangarori, tare da inganta tsarin masana'antu a cikin gida.

Bangare na uku ya shafi hadin gwiwar kasashe mambobin BRICS, wadda ta kasance karkashin tsarin hadin kai na daukacin kasashe masu tasowa. Ta hanyar hada karfin wadannan kasashe, za a iya daidaita tsarin kula da al'amuran kasa da kasa, don ya zama mai adalci.

Hakika kasashe mambobin BRICS suna da karfin tattalin arziki. Yanzu yawan GDP nasu ya kai kashi 36% na GDPn daukacin duniya, yayin da GDPn rukunin G7 da wasu manyan kasashe dake yammacin duniya, irinsu Amurka, da Birtaniya, da Faransa, da Jamus, suka kafa, bai wuce kashi 30% na adadin duniya ba. Sa'an nan idan an binciki bangaren karuwar tattalin arziki, za a ga karuwar GDPn kasashen BRICS za ta kai kashi 4% a bana, da ta fi kashi 1.7% ta rukunin G7.

Yanzu haka, bisa karfinsu na fannin tattalin arziki, kasashe mambobin BRICS na kokarin samar da damammaki ga kasashe masu tasowa, don su fitar da kansu daga kangin da kasashen yamma suka saka su, da niyyar kare ikonsu na yin babakere a duniya. Saboda haka, shugaba Xi ya jaddada a cikin jawabinsa bukatar baiwa kasashe masu tasowa karin wakilci a hukumomin kasa da kasa, da damar tofa albarkacin bakinsu kan al'amuran duniya, gami da daidaita tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa.

A nata bangare, kasar Najeriya ta sha wahalhalu sakamakon sauyawar darajar dalar Amurka, inda take bukatar gyare-gyare kan tsarin hada-hadar kudi na duniya. A sa'i daya kuma, kasar, bisa matsayinta na babbar kasa mai dimbin al'umma da karfin tattalin arziki a Afirka, na neman damar zama mai fada a ji a hukumomin kasa da kasa daban daban. Ta haka za mu iya ganin cewa bukatun kasar Najeriya da burin tsarin BRICS daya ne.

Sa'an nan a bangare na karshe, wanda shi ma yana da matukar muhimmanci, za mu ambaci cudanya a fannin al'adu. A cewar shugaba Xi na kasar Sin, ya kamata a tabbatar da kasancewar mabambantan al'adu a duniyarmu, da hakuri da juna, da koyi da juna a tsakaninsu. Ta haka ake neman daidaita tsarin da kasashen yamma suka kafa na nuna girman kai a fannin tunani da na al'adu, don baiwa kasashe daban daban damar samun 'yancin tunani, da neman hanyar raya kai da ta dace da al'adunsu. A Najeriya, al'adun kasashen yamma da tsarinsu na mulki, da 'yan mulkin mallaka suka kawo wa kasar, sun haifar da cikas ga yanayin samun ci gaban al'adun kai a kasar, tare da haddasa dimbin matsalolin dake damun kasar har zuwa yanzu. Don neman daidaita matsalolin daga asali, da samun dabarar raya kai da ta dace da al'adun kanta, Najeriya za ta iya aiwatar da karin cudanya tare da kasashe mambobin BRICS.

Idan mun takaita bayanin dake sama, za mu san cewa, shiga cikin tsarin BRICS na nufin tsaro, da ci gaban tattalin arziki, da yin tasiri a fannin al'amuran kasa da kasa, da samun 'yancin tunani, ga kasar Najeriya. Wannan nau'in alfanu shi ma ya sa tsarin BRICS ke janyo hankalin dimbin kasashe masu tasowa a kai a kai. (Bello Wang)