logo

HAUSA

Majalissar zartaswa ta Najeriya ta amince da karbo bashi domin sayen jiragen yaki guda 6

2024-10-24 10:05:45 CMG Hausa

Majalissar zartaswa ta Najeriya ta amince da karbo bashin Euro miliyan 443.3 da kuma dala miliyan 141 domin sayo jiragen yaki guda shida da alburusai ga rundunar sojin saman kasar.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Alhaji Muhammad Idiris ne ya tabbatar da hakan jiya Laraba 23 ga wata lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan da kammala taron majalissar zartaswa ta kasa a birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Ministan ya ce, gwamnati za ta samo kudaden ne daga cibiyoyin bayar da rance domin odar wadannan jiragen yaki a kokarin da ake yi na yaki da ayyukan ’yan ta’adda a kasar.

Haka kuma taron ya amince da samar da asusun bunkasa tattalin arzikin masana’antun kirkire-kirkiren fasaha da suka kunshi sha’anin fina-finai, wake-wake da raye-raye da kuma harkokin addabi.

Har’ila yau majalissar zartaswar ta Najeriya ta amince da yarjejeniyar da ta shafi ka’idojin karbar harajin ciniki da saka jari tsakanin Najeriya da yankin Hong Kong dake kasar China da kuma kasar Botswana, wadanda suka kunshi kawar da karbar haraji rubi biyu a cinikin kasa da kasa da kuma kawo karshen matsalolin kaucewa biyan haraji.

Ministan yada labaran ya ci gaba da cewa, taron majalissar na jiya Laraba ya amince da bayar da kwangilar naira biliyan 44.2 domin gina gidaje ga jami’an hukumar kwastam tare kuma da sayo motocin aiki ga hukumar.

Yayin taron shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da sauke wasu ministocinsa guda biyar sannan kuma ya nada wasu sabbi guda 7 wadanda za a tura majalissar dattawan kasar domin tantance su. (Garba Abdullahi Bagwai)