logo

HAUSA

Sin na nacewa ga matsayin bude kofa da hadin kan kasa da kasa kan kimiyya da fasaha

2024-10-24 11:30:14 CMG Hausa

 

Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya gana da wakilan masana kimiyya da fasaha na kasa da kasa da suke halartar taron dandalin raya kimiyya da fasaha na kasa da kasa na shekarar 2024 a jiya Laraba a nan birnin Beijing.

Ding ya ce, zurfafa hadin gwiwa da mu’ammalar kasa da kasa da kuma ingiza samun bunkasuwa mai dorewa ta amfani da kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha, bukatun cikin gaggawa ne wajen warware batutuwan kasa da kasa, kuma ya dace da bukatun al’ummomin kasa da kasa da na bangarorin kimiyya da fasaha. Sin za ta kara bude kofarta duba da cewa ana fuskantar hali mai sarkakiya a duniya. Sin kuma za ta nace ga matsayin bude kofa bisa adalci da daidaici da rashin nuna bambanci wajen hadin gwiwarta da sauran kasashe ta fuskar kimiyya da fasaha, da ma yin iyakacin kokarinta wajen magance wahalhalun da ake fuskanta a wannan bangare, da kuma kafa wani yanayi mai kyau na bude kofa da yin kirkire-kirkire, ta yadda za a kara more ci gaban kimiyya da fasaha, da ma amfanawa bil Adam baki daya.

Yayin ganawar tasu, masanan kimiyya da fasaha 12 daga kasashe Amurka da Turai sun bayyana niyyarsu ta hadin kai da bude kofa, suna fatan zurfafa cudanya da Sin don samar da karin ci gaba tare, da ma ingiza bunkasuwar duniya mai dorewa tare. (Amina Xu)