logo

HAUSA

Taron BRICS na wannan karo ya shaida himmar kasashe mambobin kungiyar wajen ingiza zaman lafiya a duniya

2024-10-24 16:17:11 CMG Hausa

Ga duk mai bibbiyar yadda babban taron kolin kungiyar BRICS ya gudana a birnin Kazan na kasar Rasha a ’yan kwanakin nan, ba zai gaza lura da yadda shugabannin kasashe mambobin kungiyar ta BRICS, suka mayar da hankali ga tattauna batutuwan da suka shafi wanzar da zaman lafiya tsakanin sassan kasa da kasa ba.

An dai ga yadda shugabannin kasashe mahalarta taron suka rika ganawa da juna bi da bi, kuma kusan a duk ganawa, sai sun tabo batutuwan da suka shafi dakatar da bude wuta, da kai zuciya nesa, da aiwatar da matakan shawo kan riciki, da tabbatar da wanzuwar zaman lafiya mai dorewa. Baya ga batun yiwa ayyukan MDD kwaskwarima, ta yadda za a kara jin amon sauran sassan duniya bisa mataki na adalci, da yin tafiya tare da dukkanin sassa.

Mun ga yadda shugabannin BRICS suka yi Allah wadai da duk wasu nau’o’in ayyukan ta’addanci, da nuna fin kardi ko danniya, suna masu kira da a rungumi cikakkiyar yarjejeniyar yaki da ta’addanci ta MDD. 

Yayin da ake kawo karshen taron, sanarwar da aka fitar ma ta mayar da hankali ga zakulo dabarun magance tashe-tashen hankula da ake fuskanta a sassan duniya daban daban, kama daga na Gabas ta Tsakiya zuwa na Ukraine. Inda shugabannin kasashe mambobin kungiyar suka bayyana matukar rashin jin dadin wanzuwar tashe-tashen hankula a zirin Gaza, tare da yin kira da gaggauta kaiwa ga tsagaita wuta, da ganin bayan tashin hankalin ba tare da bata lokaci ba. 

Ko shakka babu, tattaunawar shugabannin kungiyar BRICKS, da shawarwarin da suka gabatar, da ma sanarwar taron na wannan karo, su shaidawa duniya alkiblar wannan kungiyar mai matukar tasiri, na ganin duniya ta zauna lafiya, kuma al’ummunta sun rayu cikin walwala da lumana. Kuma tabbas, hakan ya dace da kudurorin al’ummun duniya masu kaunar zaman lafiya, da ci gaban kyakkyawar zamantakewar bil adama ta bai daya. (Saminu Alhassan)