logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun kaddamar da shirin horar da kwararrun likitocin jijiyoyin zuciyar dan Adam na kasa da kasa

2024-10-24 14:45:58 CMG Hausa

A halin yanzu ana aiwatar da shirin horar da karin kwararrun likitocin kasa da kasa a fannin kula da jijiyoyin zuciyar dan Adam a birnin Xiamen na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin, ta yadda za su samu damar karo ilmomi a fannin jijiyoyin zuciya, tare da yin amfani da su don kyautata lafiyar dan Adam a duk fadin duniya.