logo

HAUSA

Daga Talauci Zuwa Wadata: Kasar Sin Na Son Taimakawa Afirka

2024-10-23 08:21:58 CGTN Hausa

A ranar 25 ga Fabrairun 2021 ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin ta samu cikakkiyar nasarar kawar da fatara. Yayin da aka fitar da mazauna karkara miliyan 98.99 na karshe daga kangin talauci. Wannan gagarumar nasara ba wai kawai ta taimaka wajen cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya ba, har ma da baiwa kasar damar cimma burin farko na ci gaba mai dorewa na Majalisar Dinkin Duniya na "kawo karshen talauci a duk fadin kasar", shekaru 10 kafin lokacin da aka tsara. Kuma a ranar 17 ga Oktoban shekarar 2024 ne aka yi bikin ranar yaki da fatara ta kasar Sin karo na 10, wacce ta zo daidai da ranar kawar da talauci ta duniya karo na 32. Kamar kullum, kasar Sin tana more nasarar da samu wajen kawar da talauci baki daya a kasarta da   abokiyar ci gabanta wato nahiyar Afirka. 

A shekarar 2021, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar da cewa, kasar Sin za ta kafa cibiyoyin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka na yin musayar fasahohin aikin gona na zamani, domin inganta zamanantar da aikin gona a nahiyar Afirka. Bayan shekaru uku, wato a wannan shekara ta 2024, shugaba Xi ya kara bayyana cewa, za a aiwatar da ayyukan hadin gwiwa guda 10 a cikin shekaru uku masu zuwa. 

A karkashin shirin rage fatara da bunkasa aikin gona kuwa, kasar Sin ta kaddamar da ayyukan kawar da fatara da kuma ayyukan noma guda 47, wadanda ke ba da taimakon fasaha ga Malawi, Burundi da Cote d'Ivoire. Tare da kusan ma’aikatan noma 9,000 da kwararru a fannin noma 500 da aka aika zuwa Afirka, shirin ya amfanar da kananan manoman Afirka sama da miliyan daya, wanda ya taimaka wa nahiyar wajen samun fasahohin noma na zamani. Tare da samun goyon bayan sama da kashi daya bisa uku na al'ummar duniya da Sin da Afirka ke wakilta, da jajircewa daga gwamnatocinsu, hadin gwiwar Sin da Afirka kan kawar da fatara zai yi tasiri sosai a kokarin da ake yi na kawar da talauci a duniya. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Saminu Alhassan)