logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a yi kokarin dakatar da daukar matakan tilastawa na bangare daya

2024-10-23 10:17:49 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong ya bayyana a jiya Talata cewa, kasashe masu tasowa na ci gaba da fadawa cikin matakan tilastawa na bangare daya, wadanda ke haifar da barna, har ma da yin barazana ga rayuwa, yana mai kira da a yi kokarin dakatar da irin wannan haramtacciyar aiki gaba daya.

Da yake gabatar da sanarwar hadin gwiwa a madadin kasashe 28 mambobin MDD a kwamiti na uku na babban taron MDD karo na 79, Fu Cong ya yi bayani da cewa, “Muna sake jaddada adawarmu ga matakan tilastawa na bangare daya, kuma muna kira ga kasashe masu daukar matakan sanya takunkumi bisa radin kai da su gaggauta dakatar da irin wannan aikin gaba daya. Wakilin Sin yana mai kira ga kasashe mambobin MDD, da tsarin MDD, da sauran kungiyoyin kasa da kasa da su goyi bayan kasashen da ke karkashin wadannan haramtattun ayyuka, kuma su taimaka musu rage wahalhalu.

Fu Cong ya kuma jaddada cewa, halin da ake ciki a halin yanzu yana bukatar goyon baya da hadin kai, a maimakon adawa da rarrabuwar kawuna, don tinkarar kalubalen duniya da sa kaimi ga kare hakkin bil'Adama ga kowa da kowa. (Yahaya)