Kasashe fiye da 100 sun nuna goyon baya ga matsayin Sin na adalci a MDD
2024-10-23 20:02:54 CMG Hausa
Yau Laraba, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Lin Jian ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum, inda ya bayyana cewa, a gun taron kwamiti na uku na babban taron MDD karo na 79 da aka gudanar a kwanan nan, Pakistan ta fitar da jawabi a madadin kasashe fiye da 80, inda ta ce, harkokin jihar Xinjiang da Xizang harkoki cikin gida ne na Sin, tana adawa da tsoma baki cikin harkoki cikin gida na Sin bisa zargin kare hakkin dan Adam. Sauran kasashe sama da 20 su ma sun nuna goyon baya ga kasar Sin ta hanyoyi daban daban.
Ban da hakan, yayin da aka ambaci batun makamashi, Lin Jian ya ce, canjin makamashin duniya ya kamata ba wai kawai ya zama "labari na kasar Sin" ba, har ma da "labarai na duniya" na hadin kai tsakanin dukkan kasashe. Ra’ayin ba da kariya ga cinikayya da ra’ayin bangaranci da kuma daukar abubuwa a matsayin batutuwan siyasa, za su gurgunta moriyar al’ummar kasa da kasa.
Game da yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, Lin Jian ya bayyana cewa, bangaren Sin na adawa da cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaro da mallakar cikakkun yankunanta na Lebanon, yana fatan bangarorin da abin ya shafa za su koma hanyar warware ta siyasa da wuri.(Safiyah Ma)