Tsarin abinci na duniya PAM ya samar da taimakon abinci ga mutane miliyan 1 a Burkina Faso
2024-10-23 16:10:31 CMG Hausa
A ranar jiya Talata 22 ga watan Oktoban shekarar 2024, tsarin abinci na duniya na MDD, PAM ya sanar da samun tallafin kudi na dalar Amurka miliyan 124 daga kungiyar jin kai ta gwamnatin Amurka USAID domin magance matsalar jin kai ga mutane miliyan guda a Burkina Faso.
Daga Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.
Wannan taimako yana wakiltar kashi 70 cikin 100 na gudunmawar dukkan masu hannu da shuni na cibiyar PAM a Burkina Faso a shekarar 2024, dake kunshe da dalar Amurka miliyan 99 domin taimakon abinci, kana dalar Amurka miliyan 25 ga ayyukan jiragen sama na jin kai na MDD, in ji sanarwar PAM.
A wannan lokaci da duniya take fama da rigingimu dake karuwa, wannan tallafi ya baiwa tsarin abinci na duniya PAM damar kai ga al’umomi dake cikin bukata a wurare daban daban masu matukar wahala wajen zuwa dake kasar Burkina Faso, in ji Sory Ouane, wakilin PAM a Burkina Faso.
Kusan mutane miliyan uku suke bukatar taimako. Inda a shekarar 2024, ana kiyasta cewa mutane miliyan 2.7 kimanin kashi 12 cikin 100 na al’umma suka samu taimakon abinci na gaggawa daga watan Juni zuwa watan Augusta, a cewar rahoton PAM.
Wannan jin kai, tsarin abinci na duniya PAM ya kai ga mutane fiye da miliyan guda na mata da maza da yara da suka fi shiga hadari ta dalilin karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.