logo

HAUSA

Kasar Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-19 na dakon ‘yan sama jannati

2024-10-23 10:42:15 CMG Hausa

Hukumar lura da ayyukan sama jannati ta kasar Sin CMS ta bayyana a ranar Talata cewa, an kai hadakar kumbon Shenzhou-19 na dakon ‘yan sama jannati da rokar dakon kaya ta Long March-2F zuwa yankin harba kumbuna.

Hadakar kumbon Shenzhou-19 na da tsayin kusan mita 60 da nauyin tan 40, kuma tana jiran gudanar da wannan aikin saboda ta kasance wadda takewa aikin kumbon Shenzhou-18 baya.  

A cewar hukumar kula da harkokin binciken sararin samaniya ta kasar Sin CMSA, filin harba kumbunan da kayan aikin duk suna cikin yanayi mai kyau. Bayan jigilar kumbon da aka yi a tsaye, za a gudanar da gwaje-gwaje daban daban kamar yadda aka tsara.

Ana sa ran harba kumbon a cikin kwanaki masu zuwa. (Yahaya)