logo

HAUSA

Sakatare janar na MDD ya yi Allah wadai da asarar rayukan da ake ci gaba da yi a Gaza

2024-10-22 14:51:20 CMG Hausa

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi Allah wadai da asarar rayuka da ake ci gaba da yi a zirin Gaza, gami da hare-haren da Isra’ila ta kai kan wani gida da ke Beit Lahiya a ranar Asabar.

Mataimakin kakakin sakatare janar na MDD Farhan Haq ne ya bayyana hakan jiya Litinin a wani taron manema labarai na yau da kullun. Inda ya ce, “Dole ne a mutunta fararen hula da kuma kare su a kowane lokaci.”

Kazalika, hukumomin lafiya na Gaza sun tabbatar da cewa, Falasdinawa 87 ne aka kashe yayin da wasu fiye da 40 suka jikkata a ranar Asabar din bayan da jiragen saman yakin Isra’ila suka kai farmaki a wata unguwa a Beit Lahia da ke arewacin Gaza.

Haq ya kara da cewa, babban jami’in na MDD ya ce yana cikin matukar firgici game da tabarbarewar al’amura ga fararen hula a arewacin Gaza, gami da raba dimbin jama’a da muhallansu da ake yi, da kuma rashin muhimman abubuwan rayuwa. (Yahaya)