logo

HAUSA

Sin: Kamata ya yi a raya kimiyya da fasaha tare da kayyade kalubalolin da za su haifar

2024-10-22 13:50:30 CMG Hausa

Wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Fu Cong ya gabatar da jawabi a jiya Litinin a gun muhawara kan amfanin da bunkasuwar kimiyya da fasaha ke yiwa zaman lafiya da tsaron duniya da kwamitin sulhu na majalisar ya gudana, inda ya ce, kimiyya da fasaha kamar wani takobi ne mai kaifi biyu, shi ya sa kamata ya yi a daidaita dangantaka tsakanin samun bunkasuwa da tabbatar da tsaro da karawa aikin yin kirkire-kirkire kwarin gwiwa da sarrafa kalubaloli, ta yadda kimiyya da fasaha za su amfanawa al’ummomin kasa da kasa.

Fu ya kara da cewa, bunkasuwar kimiyya da fasaha na samar da damammaki masu kyau a mabambantan sana’o’i tare da amfanawa Bil Adama, kuma ta kawo sabon kalubale ga zaman lafiya da tsaron duniya. Wasu kasashe sun matsa lamba da dakile kamfanoni masu nazarin kimiyya da fasaha na sauran kasashe bisa hujjar magance kalubaloli. Ainihin burinsu shi ne yin babakere ta fuskar fasaha da hana bunkasuwar saura.

Game da batun daidaita aiki kimiyya da fasaha, Fu ya ba da shawarwarin Sin guda 3, na farko amfani da kimiyya da fasaha bisa doka da ka’idar kasa da kasa. Na biyu taimakawa kasashe masu tasowa a wannan fanni ta yadda za a more bunkasuwa tare. Na uku, tabbatar da cewa sarrafa fasahohin kwaikwayon tunanin dan Adama ko AI na hannun mutum ko da yaushe. (Amina Xu)