logo

HAUSA

Hukumomin kiwon lafiya na kasar Nijar sun bayyana damuwa kan raguwar ajiyar alluran yaki da cutar kwalara a duk duniya

2024-10-22 10:11:20 CMG Hausa

A ranar jiya Litinin 21 ga watan Oktoban shekarar 2024, hukumomin kiwon lafiya na kasar Nijar suka bayyana damuwa, game da labarin kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS kan cewa tun a ranar Juma’a 18 ga watan Oktoban shekarar 2024, da ajiyar alluran yaki da cutar kwalara ta ragu.

Daga birnin Yamai abokin aikinmu Mamane Ada, ya aiko mana da wannan rahoto. 

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya OMS ta nuna cewa tsakanin ranar 1 ga watan Satumban shekarar 2024 zuwa ranar 14 ga watan Oktoban shekarar 2024, fiye da kwalaben magani miliyan 8 kasashe da dama suka bukata, daga cikinsu akwai kasar Nijar. Amma sai dai fiye da kwalaben magani miliyan 7 da rabi bisa miliyan 8 aka samu aikawa cikin wadannan kasashe.

Wannan karancin alluran yaki da cutar amai da gudanawa ta kwalara, ya zo a yayin da fiye da mutane dubu 400 suka harbu da kwalara a duniya, kana fiye da mutane dubu uku suka mutu sanadiyyar cutar amai da gudanawa a wannan shekarar 2024.

A cewar, hukumomin kiwon lafiya na kasa, cikin wani rahoton watan da ya gabata, cutar kwalara ta bayyana a yankunan Tahoua, Maradi da Zinder, haka kuma mutane 705 suka harbu yayin da mutane 17 suka kwanta dama.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.