logo

HAUSA

Sin za ta kara kyautata manufofin dauke Biza don saukakawa karin mutane shiga kasar

2024-10-22 19:53:14 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce Sin za ta ci gaba da aiwatar da karin manufofi da tsare tsare, na baiwa ‘yan kasashen waje masu bukatar shiga kasar damar yin hakan, ba tare da neman Biza ba.

Lin Jian ya bayyana hakan ne a Talatar nan, yayin taron manema labarai da aka saba shiryawa, lokacin da yake tsokaci kan furucin wata kafar watsa labarai ta ketare, wadda ta ce jerin matakan na kasar Sin, da suka hada da bude kofar biyan kudade ta yanar gizo, da damar magana da harsunan waje, da hidimomin sufuri masu sauri ga baki, suna saukakawa karin masu ziyartar kasar Sin.

Jami’in ya ce ko shakka babu, kasar Sin za ta ci gaba da inganta wadannan matakai, don cin gajiyar masu ziyara, da baki dake son zama a kasar Sin. Kuma mahukuntan kasar na farin ciki da karin adadin masu ziyartar kasar.

A cewar Lin, alkaluman kididdiga na baya bayan nan, sun nuna a rubu’i na uku na shekarar bana, adadin baki masu shigowa kasar Sin ya kai mutane miliyan 8.186, karuwar kaso 48.8 bisa dari a shekara. Cikin wannan adadi kuma, mutane miliyan 4.885 sun shiga kasar Sin ne ba tare da bukatar Biza ba, adadin da ya karu da kaso 78.6 bisa dari a shekara. (Saminu Alhassan)