logo

HAUSA

Shirin Kara Karfin Afirka Na Samun Cigaba Mai Dorewa Na Zubar Da Sabon Jini Ga Aikin Hadin kan Sin Da Afirka

2024-10-21 16:52:53 CMG Hausa

 

A kan bangon ginin kwalejin ba da ilmin sana’o’i ta tarayyar Habasha, akwai wani babban allon dake dauke da jar rubutun kalmomi na Luban Workshop (ma’ana: cibiyar koyar da ilmin sana’o’i ta Luban), wanda ke jawo hankalin mutane sosai. Bayan an shiga ajujuwan Luban Workshop, ana iya ganin yadda malamai ‘yan Afirka da kasar Sin ta ba su kwasa-kwasan horarwa ke koyar da dalibansu ilmin sarrafa mutum-mutumin inji.

A cikin wannan Luban Workshop mai fadin murabba’in mita fiye da dari takwas, akwai sassan koyarwa daban daban, kamar su sashen karatu mai hanyoyin sadarwa da dama, sashen nazari da koyarwa, sashen koyar da ilmin sarrafa na’urorin masana’antu, sashen koyar da ilmin na'urori masu gano ababe, sashen koyar da ilmin mutum-mutumin injin masana’antu, da kuma na koyar da ilmin tsarin sassan kayan laturoni, inda kuma ake ajiye kayayyakin koyarwa na zamani bisa fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI. Madam Muferiat Kamil Ahmed, ministar kwadago da fasahohin sana’a ta kasar Habasha ta taba yi wa Luban Workshop yabon cewa, cibiyar ta samar da dandali mafi kyau na koyar da ilmin mutum-mutumin injin masana’antu a duk fadin kasar, wanda zai taimaka wa Habasha sosai wajen horar da nagartattun kwararru a fannin masana’antu.

Alal hakika, ban da kasar Habasha, an kafa cibiyar koyar da ilmin sana’o’i ta Luban Workshop a kasashen Afirka da dama. Tun bayan da aka fara aikin Luban Workshop ta farko a kasar Djibouti a shekarar 2019, ya zuwa yanzu ma dai, kasar Sin ta riga ta kafa cibiyoyin Luban Workshop fiye da goma a kasashen Afirka daban daban, inda ta hada gwiwa tare da kasashen ta fuskar koyar da ilmin sana’o’i, bisa aniyar taimaka musu wajen samun ‘yan Afirka masu rike da fasahohin masana’antu.

Sashen koyar da fasahohin layin dogo da aka kafa a Luban Workshop na kasar Djibouti ya cika gibin kasar a wannan fannin, inda dalibai guda 24 na rukunin farko suka riga suka fara aikinsu a kan layin dogo dake tsakanin Addis Ababa da Djibouti. A kasar Masar ma, Luban Workshop ta koyar da dalibai ilmin da ke da nasaba da gyaran motoci. A kasar Kenya ma, Luban Workshop ta hada gwiwa tare da wasu kamfanonin yanar gizo na kasar Sin, a kokarin horar da kwararru mazauna wurin ta fuskar sadarwa. A kasar Ruwanda, dalibai 30 na Luban Workshop ba ma kawai sun samu damar karatu a kwalejin koyar da masana’antu ta Ruwanda ba, har ma an ba su damar zuwa kwalejin koyar da ilmin sana’o’i na garin Jinhua a lardin Zhejiang da ke gabashin kasar Sin domin karo ilmi. Hakan ana iya ganin cewa, yayin da Luban Workshop ke sa kaimi ga ci gaban aikin koyar da fasahohin sana’o’i na kasashen Afirka daban daban, ita ma ta zubar da sabon jini ga masana’antun kere-kere da kimiyya da fasaha na Afirka.

Taimaka wa Afirka wajen samun karin kwararru wani babban mataki ne da kasar Sin ke dauka a ko da yaushe. A gun taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin kan Sin da Afirka wato FOCAC da aka yi a watan Nuwamban shekarar 2021, kasar Sin ta gabatar da manyan shirye-shirye guda 9 da take son hadin kai tare da Afirka wajen gudanarwa, ciki har da shirin kara karfin Afirka na samun dauwammen cigaba, wanda ya hada da aikin taimaka wa Afirka wajen gina da gyara makarantu goma, aikin gayyato kwararrun Afirka dubu goma zuwa kasar Sin don halartar tarurukan kara wa juna sani, aikin hadin kan Sin da Afirka ta fuskar ilmin sana’o’i mai taken Afirka Na Nan Gaba, aikin ba da saukin samun guraben aikin yi ga dalibai masu karo ilmi a kasar Sin, da dai sauransu.

A watan Agusta na shekarar bara, an kira taron tattaunawa tsakanin shugabannin Sin da Afirka a yayin taron ganawa karo na 15 na shugabannin kasashe mambobin BRICS a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu. Bayan taron, bangaren Sin ya gabatar da matakai uku na mara bayan Afirka wajen samun dunkulewa da zamanintarwa, Shirin Hadin Kan Sin da Afirka Wajen Horar Da Kwararru yana daya daga cikinsu. Shirin da ya jaddada cewa, muhimmin aikin farfado da Sin da Afirka shi ne yadda za a sauya mutanensu masu dimbin yawa zuwa ‘yan kwadago masu rike da fasahohi, ta yadda za su taimaka wa kasashensu wajen samun zamanintarwa. Don haka, kasar Sin za ta kara hadin gwiwa tare da kasashen Afirka wajen kara karfinsu a fannonin musayar fasahohi da aikin koyarwa.

Kamar yadda Sinawa kan ce, koyar da dabarun kamun kifi ya fi bayar da kifaye kai tsaye. Idan aka duba cibiyar Luban Workshop da ke mai da hankali kan koyar da fasahohi, da Kwalejin Confucius da ke dora muhimmanci kan cudanyar al’adu daban daban, da shirin hadin kan jami’an Sin da Afirka 100, da shirin kyautata kwarewar malaman makaranta bisa shawarar “Ziri Daya Da Hanya Daya”, da kuma aikin horaswa ga ‘yan Afirka dubu goma da ke iya harshen Sinanci da fasahohin sana’a dukka, to za a gane cewa, hadin kan Sin da Afirka ta fuskar kara karfin Afirka a fannoni daban daban na kara azama ga Afirka wajen samun bunkasuwa mai dorewa.

Ko da yaushe Sin na gudanar da ayyukan hadin kai tare da Afirka ne bisa bukatun Afirka na zahiri kuma bisa ra’ayin girmama juna. Kana bisa hakikanin yanayin da Afirka ke ciki na samun yawan matasa da yawan masu karancin ilmi, kasar Sin ta gudanar da ayyuka daban daban na a zo a gani bisa kyawawan sakamakon da ta samu ta hanyar amfani da ‘yan kwadago yadda ya kamata, a kokarin taimaka wa Afirka wajen samun karin kwararru a fannoni daban daban. Kana yayin da Sin ta dukufa a wannan fanni, ta mutunta hanyoyin da kasashen Afirka suka zaba, ba ta gindaya ko wani sharadin siyasa ba. Lamarin da ya samu amincewa sosai daga wajen kasashen Afirka, kana ya aza harsashi mai inganci ga hadin kan Sin da Afirka cikin dogon lokaci.

A gun taron koli na dandalin FOCAC da aka yi a birnin Beijing a farkon watan Satumban bana, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da manyan shirye-shirye goma na hadin gwiwar Sin da Afirka don neman samun zamanintarwa. A cikinsu, akwai wani babban shirin da ya shafi cudanyar al’adu, inda aka nuna cewa, kasar Sin za ta inganta shirin koyar da ilmin sana’o’i mai taken Afirka Na Nan Gaba, da gina kwalejin fasahohin injiniya, da kuma kafa cibiyoyi goma na Luban Workshop. Ban da wannan kuma, kasar Sin za ta samar wa mata da matasan Afirka dubu 60 damar zuwa kasar don karo ilmi.

Ko shakka babu, a karkashin inuwar shawarar samun bunkasuwar duk duniya da ra’ayin raya makomar bil Adama ta bai daya da kasar Sin ta gabatar, hadin kan Sin da Afirka ta fuskar kara karfin Afirka na samun bunkasuwa mai dorewa na sai kaimi sosai ga yunkurin raya makomar bangarorin biyu ta bai daya. Irin hadin gwiwa na mayar da jama’a a gaban komai tare da dora muhimmanci kan cigabansu daga dukkan fannoni, inda kowa da kowa ke iya samun dama mai adalci na samun bunkasuwa da cimma buri. Ana da imanin cewa, wadannan kananan burikan za su kasance muhimmin sabon karfi na hadin gwiwar Sin da Afirka. (Kande Gao)