logo

HAUSA

Ministan lafiya na kasar Guinea-Bissau ya yabawa tawagar likitocin kasar Sin da suka ba da gudummawa

2024-10-21 10:07:11 CMG Hausa

Ministan lafiya na kasar Guinea-Bissau Pedro Tipote, a jiya Lahadi ya nuna jin dadinsa ga ci gaba da kokarin da tawagar likitocin kasar Sin ke yi a kasar, inda ya bayyana babbar gudummawar da suke bayarwa wajen inganta kiwon lafiya da kyautata zaman rayuwar jama’ar Guinea-Bissau.

A yayin ganawarsa da kwararru daga kwalejin koyon aikin likitanci na lardin Sichuan na kasar Sin, Tipote ya jinjinawa muhimmiyar rawar da tawagar likitocin kasar Sin ta taka wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya. Mambobi hudu na tawagar za su ba da tallafin fasaha na musamman da na likitanci ga asibitin yankin Canchungo da ke da nisan kilomita 72 daga arewacin Bissau, babban birnin kasar Guinea-Bissau.

Kasar Sin ce ta ba tallafin kudade tare da gina wannan asibitin, wanda ya kasance ginshikin kula da lafiya a kasar Guinea-Bissau tun lokacin da aka kafa shi a shekarar 1977, sa’annan ta ke tura jami'an kiwon lafiya na kasar Sin zuwa asibitin a kai a kai. (Yahaya)