logo

HAUSA

Sudan da Sudan ta Kudu sun tattauna batun dawo da sufurin mai

2024-10-21 10:59:46 CMG Hausa

A jiya Lahadi ne Sudan da Sudan ta Kudu suka jaddada bukatar magance matsalolin da ake fuskanta don dawo da jigilar man da Sudan ta Kudu ke fitarwa ta yankin Sudan.

Wannan dai ya zo ne bayan da shugaban majalisar rikon kwarya ta Sudan kuma babban kwamandan sojojin Sudan ko (SAF) Abdel Fattah Al-Burhan ya gana a ranar Lahadin da ta gabata, da mai baiwa shugaban kasar Sudan ta Kudu shawara kan harkokin tsaron kasa, Tut Gatluak, a Port Sudan, babban birnin jihar Red Sea dake gabashin Sudan.

Gatluak a cikin wata sanarwar da ya fitar, ya ce "Dukkan kungiyoyin kwararru na kasashen biyu a shirye suke su kara yawan mai da ake samarwa, da kuma tabbatar da jigilar mai ta tashar ruwan Bashayer ta kasar Sudan," inda ya bayyana shirin Sudan ta Kudu na aiwatar da matsayar da aka cimma tare da gwamnatin Sudan.

Gatluak ya kara da cewa, ana sa ran gudanar da ganawa tsakanin ma'aikatun makamashi da man fetur na kasashen biyu dangane da wannan batu, yana mai cewa, "mai wata hanyar rayuwa ce ga al'ummomin kasashen biyu."

A watan Maris ne gwamnatin Sudan ta sanar da dakatar da jigilar man da Sudan ta Kudu ke fitarwa ta yankunan Sudan saboda matsalar layukan sufuri. (Yahaya)