logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu a hare-haren da Isra'ila ta kai a Lebanon ya kai 2,464

2024-10-21 09:41:40 CMG Hausa


Ma'aikatar lafiya ta kasar Lebanon ta sanar a jiya Lahadi cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon hare-haren da Isra'ila ta kai kan kasar Lebanon tun barkewar rikicin Isra'ila da kungiyar Hizbullah ya kai 2,464, tare da jikkata wasu 11,530.

Ma'aikatar ta ce, a ranar Asabar kadai mutane 16 ne suka mutu, sa'an nan wasu 59 suka jikkata. Ta kuma bayyana cewa, an kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 27 a yankin kudanci, yayin da aka kashe 5 tare da jikkata 23 a yankin Nabatieh, haka ma yankin Bekaa ya ba da rahoton karin mutane 9 da suka jikkata.

Tun daga ranar 23 ga watan Satumba ne sojojin Isra'ila ke ci gaba da kai munanan hare-hare ta sama kan kasar Lebanon a wani mataki na ci gaba da murkushe kungiyar Hizbullah.

Kungiyar Hizbullah da sojojin Isra'ila dai sun fara musayar wuta a kan iyakar Lebanon da Isra'ila ne tun a ranar 8 ga watan Oktoban shekarar 2023, yayin da ake fargabar fadadar rikicin a daidai lokacin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Hamas da Isra'ila a zirin Gaza. (Yahaya)