logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci ’yan kasar da suke zaune a kasashen waje da su dawo domin bada gudummawa wajen gina kasa

2024-10-21 11:11:42 CMG Hausa

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bukaci ’yan kasar da suke zaune yanzu haka a kasashen ketare da su dawo gida domin ci gaba da bayar da gudummawarsu wajen gina kasa.

Shugabar hukumar lura da ’yan Najeriya da suke zaune a kasashen waje Mrs Abike Dabiri-Erewa ce ta yi kiran a karshen makon jiya a wajen bikin yaye dalibai karo na 12 na jami’ar Afe Babalola dake garin Ado-Ekiti, fadar gwamnatin jihar Ekiti a kudancin kasar.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Mrs Abike Dabiri-Erewa ta ce, ’yan Najeriya da suke a waje yanzu haka, suna da gagarumar gudummawar da za su taka wajen maganin kalubale da tattakin arzikin Najeriya da na zamantakewar kasar ke fuskanta.

Ta ce, akwai matukar bukatar kwararru ’yan Najeriya da suke kasashen katare da su yi amfani da irin kwarewar da suke da ita wajen taimakawa gwamnatin Najeriyar a kokarin da take yi a yanzu haka na dora tattalin arzikin kasar kan ginshikin ci gaba mai dorewa.

Shugabar hukumar ta ce, ko kadan bai dace ba Najeriya ta ci gaba da dogaro da baki wajen gina kasa, inda ta ce, hukumar da take jagoranta ta fitar da tsare-tsare ingantattu da za su samar da damarmaki ga ’yan kasar da suke zaune a kasashen waje ta hanyar shiga aikace-aikacen da za su amfani rayuwar al’ummar kasa baki daya.

Mrs Abike ha’ila yau ta ce, ya zama wajibi Najeriya ta nemi hadin kan al’umominta da suke zaune a kasashen waje ganin cewa akwai bangarori da dama na ci gaban rayuwa da aka bar Najeriya a baya, kuma muddin ana son cike wannan gibi dole ne kowa ya shigo a dama da shi. (Garba Abdullahi Bagwai)