Yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jiragen kasa a watan Janairu zuwa Satumban bana a Sin ya kai sabon matsayi
2024-10-21 11:05:25 CMG Hausa
Kamfanin jiragen kasa na kasar Sin ya ba da labari kwanan baya cewa, daga watan Janairu zuwa Satumban bana, yawan fasinjojin da aka yi jigilarsu ta jiragen kasa ya kai fiye da biliyan 3.3, adadin da ya kai sabon matsayi a tarihi, kuma ana gudanar da aikin jigilar fasinjoji yadda ya kamata.
Tun farkon wannan shekara, jiragen kasa na tafiya sau 10792 a kowace rana, wanda ya karu da kashi 9.8% bisa na makamancin lokacin bara. A cikin wadannan watanni, yawan jiragen kasa masu nasaba da yawon shakatawa da suka yi zirga-zirga ya kai 1430, matakin da ya kara azama wajen raya tattalin arzikin yawon bude ido da na tsoffi, ban da wannan kuma, yawan bakin ketare da aka yi jigilarsu ya karu sosai, inda yawan bakin ketare da jiragen kasa mai saurin tafiya tsakanin lardin Guangdong da Shenzhen da Hongkong ya yi jigilarsu ya kai kimanin miliyan 20, wanda ya karu da kashi 43.1% bisa na makamancin lokacin bara, yayin da layin dogo dake hada Sin da Laos ya yi jigilar fasinja sau dubu 190. (Amina Xu)