logo

HAUSA

Shugaban kasar Brazil ya soke tafiyarsa ta zuwa taron kolin BRICS bayan ya samu rauni a kai

2024-10-21 11:10:06 CMG Hausa

Ofishin shugaban kasar Brazil ya sanar a ranar Lahadi cewa, an kwantar da shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva a asibitin Brasilia bayan da ya samu rauni a kansa a wani hatsarin da ya faru a gidansa ranar Asabar, inda ya soke tafiyar da ya shirya zuwa Rasha domin halartar taron kolin BRICS da ke tafe.

Kungiyar za ta gudanar da taronta karo na 16 daga ranar 22 zuwa ta 24 ga watan Oktoba a birnin Kazan.

Lula da Silva, mai shekaru 78, "ba zai je taron kolin BRICS ba" saboda shawarwarin likitoci na ya guji yin doguwar tafiya a jiragen sama, a cewar ofishinsa a cikin wata sanarwa. Amma shugaban, duk da haka, zai halarci taron ta kafar bidiyo daga Brasilia. (Yahaya)