logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da shugaban kwamitin tsarin mulkin kasar Faransa

2024-10-21 15:56:42 CMG Hausa

 

Yau Litinin da safe, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya gana da shugaban kwamitin tsarin mulki, kana tsohon firaministan kasar Faransa Laurent Fabius a nan birnin Beijing.

A ganawar tasu, Wang ya ce, ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping a Faransa bana ta kasance wata ziyara ce da ta kafa sabon tarihi, matakin da ya ba da jagoranci ga raya huldar Sin da Faransa da ma Sin da Turai a manyan fannoni a sabon yanayi da ake ciki. Huldar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Turai na fuskantar wasu kalubaloli wadanda ba su dace da muradunsu ba. Yana mai fatan EU ta kara tuntuba da yin shawarwari da bangaren Sin don fidda wata hanyar da ta dace don warware abubuwan da suke jawo hankalinsu.

A nasa bangare kuwa, Fabius ya ce, nacewa ga sada zumunta tsakanin kasashen biyu tsarin diplomasiyya ne da Faransa ta dade take daukawa. Faransa ba za ta canja matsayin da ta dauka ba, wato daidaita matsaloli ta hanyar yin sulhu. (Amina Xu)