logo

HAUSA

Gwamnatin jihar Niger ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwa da wasu kamfanonin kasar Sin wajen bunkasa sarrafa kayan amfanin gona

2024-10-20 14:45:37 CMG Hausa

Gwamnatin jihar Niger dake arewa ta tsakiyar Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniyar aikin hadin gwiwa da kamfanonin gine gine na kasar Sin COVEC da kuma na CREC wajen aikin kwangilar samar da cibiyar sarrafa kayayyakin amfanin gona a jihar.

A lokacin da yake zantawa da manema labaru jim kadan da kulla yarjejeniyar a fadar gwamnatin jihar dake garin Mina a ranar juma`a 17 ga wata, sakataren gwamnatin jihar Alhaji Abubakar Usman ya ce wannan alaka za ta baiwa jihar damar kasancewa a kan gaba a fagen aiki da sabon tsarin noma na zamani a kasa baki daya.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Sakataren gwamnatin jihar ta Niger ya ce babu shakka jarin dala miliyan  684 da kamfanonin na kasar Sin suka saka ya kara dora jihar ta Niger bisa tafarkin samar da masana`antar sarrafa kayan amfanin gona da kuma kara habaka sha`anin noman abinci.

Alhaji Abubakar Usman ya ci gaba da cewa kulla yarjejeniyar wannan kwangila ya nuna a fili irin kokarin da gwamnatin jihar keyi na mayar da dukkan al`amuran ta ga sha`anin aikin gona wanda zai kara habaka kafofin samun kudaden shiga.

Har ila yau sakataren gwamnatin jihar ta Niger yace samun hadin gwiwa da kamfanonin kasar na China zai kara tallata arzikin da jihar ke da su ne ta yadda masu saka jari `yan kasa da na kasashen ketare za su nuna sha`awar yin hadin gwiwa da gwamnatin jihar. 

Shi ma da yake tofa albarkacin bakin sa a game da yarjejeniyar aikin kwangilar da aka kulla, kwamashinan kasuwanci da harkokin zuba jari na jihar Alhaji Aminu Sulaiman Takuma ya ce bayan kulla wannan alaka, wakilan gwamnatin jihar da kuma na kamfanonin biyu sun gana da tawagar bankin raya kasashen Afrika, inda suka tattauna a kan yadda za a aiwatar da tsare-tsaren samar da cibiyar rukunin masana`antun musamman na sarrafa kayayyakin amfanin gona wanda hakan zai taimaka mutuka wajen samun nasarar juya tsarin kasuwancin kayan amfanin gona a jihar zuwa matsayin kasa da kasa. (Garba Abdullahi Bagwai)