logo

HAUSA

Wani hari kan FDS ya yi sanadiyar mutuwar mutum 7 a Assamaka yankin Agadez

2024-10-20 14:47:02 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, wasu hare-hare uku a lokaci guda kan tashoshin jami’an tsaro na sojin kasa, jandarma da ’yan sanda na Assamaka mai nisan kilomita 245 daga arewa masu yammacin Arlit, yankin Agadez a ranar jiya Asabar 19 ga watan Oktoban shekarar 2024 yayi sanadiyar mutuwar mutane 7.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.  

Da misalin karfe daya na rana ne, na ranar jiya 19 ga watan Oktoban shekarar 2024 ne, wasu motoci kirar Toyota guda 6 dauke da makamai da mutune da ba’a tantance su ba, suka afkawa jami’an tsaro na FDS dake sintiri a wurare uku. Inda aka yi ta musanyar wuta na dan lokaci, kafin sojojin Nijar su samu dauki.

Lamarin da ya tilastawa maharan ja da baya, a lokacin da wani kwamandan tare da sojojinsa da kuma rundunar 23 BIA ta Assamaka dake cikin wani rangandi suka kawo dauki ga abokansu da suka shiga tsaka mai wuya.

A karshen wannan gumurzu, mutum 7 suka mutu daga cikinsu jami’an tsaro na Nijar 6 da farar hulla 1, yayin da mutane 5 suka ji rauni.

A cewar rundunar sojojin Nijar, maharan sun yi awon gaba da bindigogi kirar AK47 guda 9 da kananan bindigogi guda 3.

hedkwatar rundunar sojojin Nijar, a labarinta na baya bayan nan ta nuna cewa, an fatattaki ’yan bindigan da suka kai hari a Assamaka da kama mutane 37 daga cikinsu da ake zargi.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.