logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen kasar Sin ya gana da takwaransa na Birtaniya

2024-10-19 15:51:31 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da sakataren harkokin wajen kasar Birtaniya David Lammy, a jiya Juma’a a birnin Beijing.

Wang ya ce, kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da Birtaniya wajen bin matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da kiyaye fahimtar juna da mutunta juna, da mai da yin hadin gwiwa da bude kofa a matsayin babban jigo, da zurfafa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da sa kaimi ga yin hadin gwiwa a aikace, da daukaka dangantakar dake tsakanin Sin da Birtaniya zuwa wani sabon mataki ba tare da tangarda ba.

A nasa bangare kuwa, Lammy cewa ya yi, gwamnatin Birtaniya ta kuduri aniyar karfafa tattaunawa da hadin gwiwa tare da kasar Sin, da kuma tafiyar da bambance-bambance yadda ya kamata cikin daidaito, da mutunta juna, wanda ya dace da moriyar bangarorin biyu na dogon lokaci. Ya kara da cewa, Birtaniya na ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen mutunta kudurin da ta dauka kan batun Taiwan tun bayan kulla huldar diflomasiyya, kuma za ta ci gaba da bin ta cikin dogon lokaci. (Yahaya)